Tinubu Ya Kafa Shirin Samar da Aiki Wa Matasa, an Raba Miliyoyi a Karon Farko
- Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shiri matasa na Nigerian Youth Academy (NiYA), domin bunƙasa basira da ƙwarewa
- An gudanar da bikin ƙaddamar da shirin a Fadar Shugaban Kasa, Abuja, inda Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya wakilci Bola Tinubu
- Matasan da suka kammala gwajin shirin sun samu kyautar kudi har Naira miliyan 1 domin tallafa musu, su zama ‘yan kasuwa masu dogaro da kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ɗauki wani babban mataki wajen ƙarfafa matasa ta hanyar ƙaddamar da shirin Nigerian Youth Academy (NiYA).
Wannan shiri na musamman zai bai wa matasa damar samun ƙwarewa da horo a fannoni daban-daban domin samun ayyukan yi.

Asali: Facebook
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya wallafa yadda aka kaddamar da shirin a fadar shugaban kasa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shettima ya yaba da shirin, ya na mai cewa yana daga cikin muhimman manufofin gwamnati wajen bunƙasa matasa da tattalin arziki.
Ministan Matasa, Olawande Emmanuel Ayodele, ya wallafa cikakkun bayanai game da shirin a wani sako da ya wallafa a Facebook.
Ayodele ya ce shirin wata babbar dama ce ga matasan Najeriya don samun ƙwarewa ta yadda za su yi kafada-da-kafada da takwarorinsu na duniya.
Gwamnati za ta bunƙasa ƙwarewar matasa
Ministan Matasa, Olawande Emmanuel Ayodele, ya bayyana cewa shirin wata hanya ce ta cika alkawarin Shugaba Tinubu na samar da hanyoyin da matasa za su samu ci gaba.
Ya ce a cikin shekaru biyu masu zuwa, shirin zai taimaka wajen samar da miliyoyin ayyukan yi ga matasan Najeriya.
Matasan da suka cancanta sun samu tallafi
A yayin bikin ƙaddamar da shirin, an bayyana cewa an raba kyautar N1m ga matasa shida daga kowace shiyya ta Najeriya waɗanda suka kammala gwajin shirin.
Ministan matasa ya ce tallafin yana da nufin taimaka musu su fara sana’o’insu da kuma bunƙasa tattalin arzikinsu.

Asali: Facebook
"Shirin wata babbar dama ce ga matasa domin su koyi sana’o’in da za su dogara da kansu a rayuwa,"
- Olawande Emmanuel Ayodele
Ya kuma yi kira ga matasan Najeriya da su rungumi wannan dama tare da yin ƙoƙari wajen cin gajiyar horon.
Manyan baki da suka halarci taron
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati ciki har da Ministan Kuɗi, Wale Edun, da Ministan Kasafi da Tsare-Tsaren Ƙasa, Atiku Bagudu.
Haka kuma akwai Ministan Ma’aikata da Ayyuka, Nkiruka Onyejeocha, tare da shugabannin hukumomin gwamnati.
Baya ga hakan, akwai wakilan ƙasashen waje daga Tarayyar Turai da ofishin jakadancin Amurka da suka halarci taron don nuna goyon bayansu ga shirin.
Ministan harkokin Matasan ya nuna godiyarsa ga duk waɗanda suka ba da gudunmawa wajen kaddamar da shirin.
Rivers: An ba gwamnatin Najeriya shawari
A wani rahoton, kun ji cewa an ba gwamnatin Najeriya shawari kan yadda za ta warware rikicin jihar Rivers da aka dade ana fama da shi.
Wani dan majalisa ya bukaci Bola Tinubu ya dawo da gwamna Simi Fubara, sai ya yi aiki tare da Abdulsalami Abubakar domin warware rikicin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng