Najeriya Ta Ɗauko Hayar Jami'ai daga Ketare don Koyar da Sojoji Dabaru, Za a Cafko Turji
- Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar, ya bayyana sabon shirin da Najeriya ke yi wajen inganta tsaro a sassa daban-daban na ƙasar
- Ya bayyana cewa an shirya horas da dakarun 2,400 kan dabarun yaƙi na musamman a tunkari matsalar tsaro a bangarori da dama
- Alhaji Badaru ya ce jami'an da za su ba sojojin Najeriya horo sun fito daga ƙasashe bakwai masu ƙwarewa a dabarun yaƙi na musamman
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ministan tsaron ƙasar nan, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa Najeriya ta dauko hanyar kawar da matsalolin rashin tsaro a sassa daban-daban.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya kaddamar da aikin horas da dakarun Najeriya 800 a Jihar Kaduna, domin ƙarfafa su wajen yaƙi da 'yan ta'adda.

Asali: Facebook
RFI Hausa ta wallafa cewa Alhaji Badaru Abubakar ya ce wadannan dakarun su ne kaso na farko na jami'ai 2,400 da Najeriya za ta horas tare da haɗin gwiwar ƙwararru daga ƙasashe bakwai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin horas da sojojin Najeriya
Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Badaru Abubakar, ya bayyana cewa za a horas da jami'an tsaron ƙasar nan kan sababbin dabarun yaƙi, irin wanda ba a saba da shi yau da kullum ba.
Ya ce wannan zai ba su damar gudanar da ayyuka na musamman, gaggawar ceto waɗanda aka sace, tare da yaƙi da rashin tsaro da kwarewa.
Ya ce:
"Mun ƙaddamar da koyarwa ta musamman ga sojoji 800, waɗanda aikinsu zai kasance irin na faɗa wanda ba a saba da shi ba."
Ya ƙara da cewa horaswar da ake yi ta musamman zai taimaka musu wajen shiga irin ayyukan ƙundunbala.
Ministan tsaro ya ce ana dab da kama Turji
Muhammadu Badaru Abubakar ya bayyana cewa gwamnati a shirye take ta karɓi dukkanin ƴan bindigar da suke son tuba tare da ajiye makamai.

Kara karanta wannan
Gudaji Kazaure: Babban jigo a APC ya gana da Atiku, ya fadi shirin kifar da Tinubu
Sai dai ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta rika bin ƴan ta'adda domin lallaɓa su su zo a yi sulhu ba, don haka ba za a lamunci ƴan bindiga suna ci gaba da kashe jama'a ba.

Asali: Facebook
Ministan ya ƙara da cewa yanzu haka, dakarun Najeriya sun yi nasarar kawar da wasu manyan 'yan ta'adda, kuma Bello Turji ya na dab da shiga hannu.
"An fara samun sauƙin ta'addanci" – Badaru
Ministan ya bayyana cewa ana samun kwanciyar hankali a wasu yankunan ƙasar sakamakon yadda gwamnati ta dukufa wajen magance matsalar tsaro.
Ya ce daga cikin wuraren da a yanzu ake samun sauƙin ayyukan 'yan ta'adda akwai Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna, inda a cewarsa, an samu zaman lafiya a yanzu.
Badaru ya roƙi 'yan Najeriya kan ta'addanci
Gwamnatin ƙasar nan ta roƙi jama'a da su ba da haɗin kai domin sauƙaƙa wa jami'an tsaro aiki wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar, wanda ya yi wannan kira, ya kuma bayyana illar da ke tattare da mazauna garuruwa da ke ba da bayanan dakarun tsaro ga 'yan ta’adda.
Ya ce irin ƙaramar ribar da ake ba masu bayar da bayanai ba ta taka kara ta karya ba, amma tana jefa rayuwar jama'a cikin mummunan haɗari tare da kawo koma baya ga ayyukan sojoji.
"Karshen 'yan bindiga ya zo," Badaru
A baya, mun wallafa cewa Ministan tsaro na Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana da ƙwarin gwiwa cewa ana dab da kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga a ƙasar.
A yayin wani taro da aka yi a Katsina, Ministan ya roƙi rundunar sojojin sama ta Najeriya da su haɗa kai da sauran hukumomin tsaro domin kakkaɓe dukkanin makiyan kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng