"Za a Sha Jar Miya": Ɗan Majalisar Tarayya Ya Raba Tallafin Sama da N110m ana Shirin Sallah

"Za a Sha Jar Miya": Ɗan Majalisar Tarayya Ya Raba Tallafin Sama da N110m ana Shirin Sallah

  • Ɗan Majalisar Bakori da Ɗanja a Katsina, ya raba tallafin sama da N100m daga fara azumi zuwa yanzu da ake shirin bikin Sallah
  • An ruwaito cewa akalla mutane 500 daga kananan hukumomin Bakori da Ɗanja ne suka samu tallafin N50,000 daga Abdullahi Balarabe Dabai
  • Bayan haka kuma Hon. Abdullahi Balarabe Dabai ya raba kudi ga shugabannin jam'iyyu da ƴan siyasa domin shirin ƙaramar Sallah

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bakori/Danja, Hon.Abdullahi Balarabe Dabai, ya raba tallafin azumi da goron Sallah na kimanin Naira miliyan 110,875,000 ga al’ummar mazabarsa.

Ɗan Majalisar wanda aka fi sani da A. B Dabai ya yi rabon tallafin ne a ranar Lahadi, 23 ga watan Maris a gidansa da ke garin Dabai, a ƙaramar hukumar Ɗanja a Katsina.

Kara karanta wannan

'Dan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu ya gamu da fushin matasa, an dakawa motar tallafinsa wawa

Abdullahi Balarabe Dabai.
Dan Majalisar Bakori da Danja ya gwangwaje mutanen mazaɓarsa da tallafin sama da N110m Hoto: Hon. Abdullahi Balarabe Dabai
Asali: Facebook

Katsina Post ta tataro cewa dubban jama’a daga sassa daban-daban na mazabar sun amfana da tallafin da aka shirya domin rage wa al’umma radadin tattalin arziki a wannan wata mai alfarma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabon tallafin kayan abinci sama da N74m

Tun daga farkon watan Ramadan, Hon. A. B Dabai ya fara rabon kayan abinci ga jama’a, wanda ya kunshi, buhunan shinkafa sama da 1,500 da gero aƙalla buhuna 200.

Bayanai sun nuna cewa jimillar kudin da aka kashe wajen siyan wadannan kayayyakin abinci ya kai Naira miliyan 74.

Wadanda suka amfana da kayan abinci sun hada da shugabannin jam’iyyar PDP a matakin karamar hukuma, gunduma da wakilan akwatunan zabe.

Haka zalika ƙungiyoyin al’umma daban-daban, gidajen siyasa na kowacce jam’iyya a Bakori-Danja kamar ƴan APC suma sun amfana da tallafin, ba wai PDP kadai ba

Ɗan Majalisa ya rabawa mutane kudi

Bayan rabon kayan abinci, Hon. A. B Dabai ya kuma raba tallafin kudi ga wasu al’ummar mazabar Bakori da Ɗanja.

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

Mutane 500 daga sassa daban-daban na mazaɓar sun samu tallafin N50,000 kowannensu. Jimillar kudin da aka kashe wajen rabon wannan tallafi ya kai Naira miliyan 25.

A ranar Lahadi, an raba tallafin Naira miliyan 10,875,000 a matsayin goron Sallah ga shugabannin jam’iyyar PDP da kungiyoyin da suka bada gudunmawa wajen a tafiyar siyasar ɗan majalisar.

Daga rabon kayan abinci zuwa rabon kudade na goron Sallah, adadin kudin da Hon. A. B Dabai ya kashe domin tallafa wa al’ummar Bakori-Danja ya kai N110.875m.

Ab Dabai.
A. B Dabai ya gwangwaje jama'ar mazaɓarsa ana shirin Sallah Hoto: Abdullahi Balarabe Dabai
Asali: Facebook

Mutane sun yaba da tallafin 'dan majalisar

Ɗaya daga cikin ƴan gudauniyar A.B Dabai, Muhammad Bello ya nuna farin cikinsa bisa wanna abin arziki da ɗan Majalisa ya yi yayim hira da wakilin Legit Hausa.

"Wannan tallafin a yaba ne, muna yabawa maigidada Hon. AB Dabai kuma muna addu'ar Allah ya kara dafa masa ya ci gaba da ayyukan alheri don ba yanzu ya fara.

- In ji Muhammad.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ware 'yan APC a jiha 1, ya ba su buhunan shinkafa 7,000 saboda Ramadan

Gwamnatin Katsina ta raba tallafi a Ramadan

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Katsina karkashin Gwamna Dikko Raɗda ta raba tallafin kayan abincu ga zawarawa da marasa galihu a watan Ramadan.

Matan da suka amfana da tallafin sun fito daga kananan hukumomin Katsina, Kaita, Rimi, da Batagarawa, inda kowacce ta samu buhun shinkafa da ₦10,000.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng