Allah Sarki: Abin da Radda Ya Yi bayan Samun Labarin Rasuwar Mahaifiyarsa Yana Saudiyya

Allah Sarki: Abin da Radda Ya Yi bayan Samun Labarin Rasuwar Mahaifiyarsa Yana Saudiyya

  • Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda ya samu labarin rasuwar mahaifiyarsa lokacin da ya ke a ƙasar Saudiyya
  • Dikko Radda wanda ya je Saudi domin yin Umrah tare da iyalansa, ya dawo gida Najeriya nan-take bayan samun labarin rasuwar
  • Gwamnan ya iso gida Najeriya a ranar Litinin, 25 ga watan Maris inda ya wuce mahaifarsa domin ci gaba da karɓar ta'aziyya
  • A garinsa na Radda, gwamnan ya ziyarci makwancin ƙarshe na mahaufiyarsa wacce ta riga mu gidan gaskiya a daren ranar Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda, ya dawo gida Najeriya daga ƙasar Saudiyya.

Gwamna Dikko Radda ya dawo gida Najeriya ne bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umar Radda Baribari.

Gwamna Radda ya dawo Najeriya
Gwamna Radda ya dawo gida Najeriya daga Saudiyya Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Gwamna Dikko Radda ya baro Saudiyya

Gwamnan ya sauka a filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Mallam Aminu Kano (MAKIA) a Kano a ranar Litinin, 24 ga watan Maris 2025, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Radda ya dawo ne tare da matarsa, Hajiya Zulaihat, wasu daga cikin ƴaƴansa da kuma ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Musawa/Matazu, Hon. Abdulahi Aliyu.

Daga birnin Kano, Gwamnan ya wuce garinsu na Radda da ke ƙaramar hukumar Charanchi a jihar Katsina, inda ya haɗu da iyalansa don karɓar baki masu zuwa yi masa ta'aziyya.

A lokacin da ya isa Radda da misalin ƙarfe 2:40 na rana a ranar Litinin, ya samu tarba daga wajen mataimakinsa, Faruk Lawal Jobe.

Gwamna Radda ya ziyarci kabarin mahaifiyarsa

A wani bidiyo da babban sakataren yaɗa labaransa, Ibrahim Kaulaha Mohammed ya sanya a Facebook, an nuna gwamnan ya ziyarci kabarin mahaifiyar ta sa bayan ya isa garin Radda.

Gwamnan ya ɗuka a gaban kabarin cike da shauki inda ya yi addu'a ga mahaifiyar ta sa wacce ba rabon su gana kafin ta rasu.

Dikko Umaru Radda
Radda ya dawo Najeriya Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Idan ba a manta ba dai, Gwamna Radda ya na Saudiyya wajen gudanar da Umrah lokacin da ya samu labarin rasuwar mahaifiyarsa wacce ta rasu a daren ranar Asabar, 22 ga watan Maris 2025.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kadu kan rasuwar mahaifiyar Gwamna Radda, ya tura sako mai muhimmanci

Kafin ya baro Saudiyya, Gwamna Radda ya samu ta’aziyya daga manyan mutane da dama da ke ƙasa mai tsarki domin aikin Umrah.

Daga cikinsu akwai wasu gwamnoni, da kuma ƴan majalisar dokoki na jiha da na tarayya.

Ko a nan gidan Najeriya ma, manyan mutane sun taya gwamnan jaje kan babban rashin da ya yi a rayuwarsa.

Tinubu ya yi wa Gwamna Radda ta'aziyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi jimamin rasuwar mahaifyar gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda.

Shugaba Tinubu ya aika ga saƙon ta'aziyyarsa ga Gwamna Radda kan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara'u Umar Radda wacce ta rasu tana da shekara 93 a duniya.

Mai girma Bola Tinubu ya bayyana marigayiyar a matsayin mace ta gari wacce ta sadaukar da rayuwarta wajen taimakon al'umma.

Ya yi addu'ar Allah Ya ji ƙanta da rahama, Ya kuma ba iyalanta haƙuri da juriyar wannan babban rashin da suka yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng