Barau: An Saki Adadi da Bayanin Tantance Matasan da Suka Nemi Tallafin N5m

Barau: An Saki Adadi da Bayanin Tantance Matasan da Suka Nemi Tallafin N5m

  • Sanata Barau Ibrahim Jibrin ya ce matasa 3,110 daga jihohin Arewa maso Yamma sun nemi shiga shirin tallafin noma da ya kirkiro
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce za a bai wa matasa 558 rancen kudi tsakanin N1m zuwa N5m domin harkar noma
  • Kano ce ta fi yawan masu neman shiga shirin, sai Jigawa da Katsina, sannan za a tantance wadanda suka cancanta nan gaba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya kaddamar da shirin BIARN don habaka noma a Arewa maso Yamma.

A cewar Sanata Barau Jibrin shirin zai tallafa wa matasa 558 da rancen kudi domin shiga harkar noman shinkafa da masara.

Barau
An bayyana adadain matasan da suka nemi tallafin Barau. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Twitter

Legit ta tattaro bayanai kan yadda za a tantance matasan da suka nemi shiga shirin a wani sako da Sanata Barau ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Barau na kara barazana ga Abba a Kano, 'yan fim din Dadinkowa sun goyi bayansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barau Jibrin ya bayyana cewa Bankin Noma (BOA) ne zai kula da rancen tare da tabbatar da aiwatar da shirin yadda ya kamata.

Ya kara da cewa shirin na daga cikin kudirorinsa na farfado da noma da tallafa wa matasa, kuma yana goyon bayan ajandar shugaba Bola Ahmed Tinubu kan inganta harkar abinci.

Jihohin da suka nemi shiga shirin Barau

Sanata Barau ya bayyana cewa an samu gagarumin martani daga matasa a jihohin Arewa maso Yamma da ke son shiga shirin.

A cewarsa, Kano ce ta fi yawan masu neman shiga shirin da mutum 998, sai Jigawa 590, Katsina 455, Kaduna 397, Zamfara 240, Sokoto 221 da Kebbi 209.

Sanata Barau ya ce duk wadanda suka cike fom za a tantance su, kuma za a sanar da wadanda suka cancanta nan da mako guda.

Yadda shirin zai gudana bayan tantancewa

Kara karanta wannan

Gwamnoni 35 sun yi matsaya kan dakatar da Fubara da Tinubu ya yi

Sanata Barau ya bayyana cewa shirin zai bayar da rancen N1m zuwa N5m ga kowane matashi da aka zaba domin ya zuba jari a noman shinkafa da masara.

A cewarsa, za a kaddamar da shirin gaba daya a hukumance a wata mai zuwa, karkashin jagorancin Farfesa Bashir Mohammed Fagge.

Barau
Sanata Barau na jawabi a majalisa. Hoto: Barau I Jibrin
Asali: Facebook

Ra’ayoyin jama’a kan shirin BIARN

Matasa da dama sun bayyana ra'ayoyi karkashin sanarwar da Sanata Barau Jibrin ya fitar game da shirin.

Wani matashi mai suna Halliru Ibrahim Batagarawa ya yaba da shirin, ya na mai cewa yana fatan zai taimaka wajen samar da ingantaccen lokacin noma da bunkasa wadatar abinci.

Shi kuwa Taslim Bn Muhammad Jumuah ya bukaci Sanata Barau da ya fadada shirin zuwa sauran yankuna biyar na kasar domin duk ‘yan Najeriya su amfana.

Sai dai Bala Abdu Maitsidau ya bayyana damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke hana manoma aiki, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

An nemi kama sakataren APC kan yunkurin dakatar da gwamnan PDP a Osun

"Tallafi ba zai inganta rayuwar al'umma ba. A rage kudin mai, a rage haraji da samar da tsaro a wuraren da ake noma idan ana son kawo cigaba."

Barau ya karbi 'yan fim din Dadinkowa

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Barau Jibrin ya karbi masu shirya fim din Dadinkowa mai dogon zango.

Masu shirya fim din sun masa mubaya'a suna masu cewa sun yaba da ayyukan cigaba da Sanata Barau ke yi a majalisa da jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng