An Nemi Saka Abdulsalami Abubakar da Sarkin Musulmi a Maganar Fubara

An Nemi Saka Abdulsalami Abubakar da Sarkin Musulmi a Maganar Fubara

  • 'Dan majalisar wakilai, Awaji-Inombek Abiante, ya bukaci Bola Tinubu ya mayar da Gwamna Siminalayi Fubara kafin wa’adin dokar ta-baci ya kare
  • Ya kuma bukaci a kira kwamitin zaman lafiya na kasa karkashin jagorancin tsohon shugaba Abdulsalami Abubakar, don sasanta rikicin siyasar Rivers
  • Awaji-Inombek Abiante ya ce matakin da shugaba Bola Tinubu ya dauka a jihar Rivers ya na da kura-kurai kuma ya na iya jefa kasa cikin hadari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Tun bayan ayyana dokar ta-baci a Rivers, rikicin siyasar jihar na kara daukar hankalin al'umma.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu tare da majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

Abdulsalami
An bukaci Tinubu ya yi amfani da Abdulsalami Abubakar wajen magance rikicin Rivers. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

A wata hira da aka yi da shi a tashar Channels TV, dan majalisar tarayyar ya bukaci Shugaban kasa Tinubu ya janye dakatarwar da ya yi.

Kara karanta wannan

Dawowar Fubara: Ana rade radin yin sulhu a Rivers, Wike ya yi magana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abiante ya bukaci ba da dama ga kwamitin zaman lafiya na Abdulsalami Abubakar ya shiga tsakani.

Bukatar mayar da gwamna Simi Fubara

Awaji-Inombek Abiante, ya bukaci Shugaba Tinubu ya mayar da Gwamna Fubara kafin karewar dokar ta-baci a Jihar Rivers.

Ya ce dakatar da gwamnati mai ci na dimokuradiyya bai dace ba, kuma hakan na iya haifar da matsala ga tsarin mulkin kasa.

Ya kara da cewa matakin bai samu amincewar jama’a ba, inda mutane da kungiyoyi daban-daban suka soki shi, ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi da Femi Falana.

Har ila yau, kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) da kungiyar 'yan Neja Delta (PANDEF) sun nuna rashin amincewarsu da dakatarwar.

Fubara
Gwamnan Rivers da aka dakatar. Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Instagram

Nuna shakku kan dalilan dakatar da Fubara

Hon. Abiante ya ce akwai matsaloli a bayanan da shugaba Tinubu ya dogara da su wajen ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Rikicin Ribas: An ƙara samun bayanai kan dalilin shugaba Tinubu na dakatar da gwamna

A cewarsa, an yi ikirarin cewa Fubara bai yi kokarin sake gina zauren majalisar dokokin jihar da aka rusa ba, amma hakan ba gaskiya ba ne.

Ya ce sabon hafsan da aka nada a matsayin mai kula da jihar ya kai ziyara don duba gine-ginen da Fubara ya fara.

Haka nan, Abiante ya ce rahotannin cewa an farmaki bututun mai a jihar ba su da tushe, domin tuni aka gyara bututun mai kuma komai na tafiya yadda ya kamata.

Kira ga kwamitin zaman lafiya

'Dan majalisar ya bukaci a bai wa kwamitin zaman lafiya na kasa karkashin jagorancin Abdulsalami Abubakar damar sasanta rikicin siyasar Rivers.

Ya ce kwamitin, wanda ke da manyan mutane kamar Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad III da Matthew Hassan Kukah zai iya kawo maslaha tsakanin bangarorin da ke rikici.

An fara maganar sulhu kan dakatar da Fubara

Kara karanta wannan

"Ka da a ɗora mun laifi": Gwamna Fubara ya cire tsoro, ya ƙaryata kalaman Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin yankin Kudu maso Kudu sun fara magana domin warware rikicin jihar Rivers.

Fadar shugaban kasa da ministan Abuja, Nyesom Wike sun yi magana kan kokarin shawo kan matsalolin jihar da samar da zaman lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng