Gwamna Abba Ya Yi Buda Biki da Marayu, Ya Ɗauki Alkawarin ba Su Aikin Yi
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa zai tabbatar da jin daɗin marayu ta hanyar inganta rayuwarsu ta fuskoki da dama
- Abba ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta tallafa wa marayu wajen samun ilimi da koyon sana’o’i da sauran ababen more rayuwa a Kano
- Sannan Abba Gida Gida ya bayar da umarnin a tattaro takardun marayun da suka kammala karatu, domin a sama masu aikin yi a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jaddada aniyarsa ta tabbatar da jin daɗin marayu dake zaune a sassa daban-daban na jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa zai cin ma hakan ne ta hanyar inganta ababen more rayuwa, ayyukan ci gaban jama'a da ayyukan jin ƙai.

Asali: Facebook
Wannan na kunshe a sanarar da babban sakataren yaɗa labaran gwamna, Mustapha Muhammad, ya fitar a ranar Lahadi, kuma aka wallafa a shafin Facebook na darektan yada labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya yi wannan jawabi ne yayin wani liyafar buda-baki da aka shirya tare da marayu a fadar gwamnatin Kano a yammacin Lahadi.
Gwamna Abba zai cicciba marayu a Kano
Da yake jaddada muhimman abubuwan da gwamnatinsa ke mayar da hankali a kai, Gwamna Abba ya ce ilimi na da matuƙar muhimmanci, wanda ya sa shi sanya dokar ta baci a bangaren.
Ya tabbatar wa marayu cewa gwamnatinsa za ta tallafa masu wajen samun ilimi, har su kai ga yin karatu a jami’o’i ko wasu manyan makarantu.

Asali: Facebook
Ya ce:
"Za mu kuma tallafa wa waɗanda ke da sha’awar koyon sana’a. Muna da makarantu 26 na koyon sana’o’i, kuma bayan sun kammala, za mu ba su kayan aikin da suka dace da sana’ar da suka koya."
Gwamnatin Abba za ta taimaka wa mata
Gwamnan ya kuma ambato yadda ake ci gaba da raba tallafin N50,000 ga mata a faɗin jihar, wanda ya bayyana a matsayin shiri na musamman don tallafa wa mata.
Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin faɗaɗa wannan tallafi ga mata da ke gidan marayu, domin inganta rayuwarsu.
A bangaren ababen more rayuwa, gwamnan Kano ya yi alkawarin gina ɗakin kwana na zamani da kayan more rayuwa ga marayu, wanda zai haɗa da gadaje da kuma filin wasanni.
"Za mu ba marayu aiki" — Gwamna Abba
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kuma bayar da umarni da a tattara sunayen marayu da suka kammala karatu waɗanda ke neman aiki domin a ba su aikin yi.
Ya ce:
"A kwanan nan mun bayar da guraben aiki kai-tsaye ga ɗalibai 54 da suka dawo daga Indiya. Me zai hana mu miƙa irin wannan tallafi a gare ku?"

Kara karanta wannan
Duniyar fina finan Najeriya ta yi rashi, fitacciyar jaruma ta rasu bayan mata tiyata
A cikin shirin tallafawa marayu, gwamnan ya kuma ba da kyautar guraben aikin hajji biyu ga marayu don sauke farali.
Abba ya ba hadimansa umarnin bayyana kadarorinsu
A baya, kun samu labarin cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci dukkanin hadiman siyasa da ya nada da su bayyana kadarorinsu a gaban hukumar da'ar ma’aikata ta kasa.
Wannan umarni ya zo ne a bayan koken hukumar CCB, gwamnan ya ce bayyana yawan kadarorin zai taimaka wajen dakile duk wata matsala da za ta iya taso wa a nan gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng