Fubara Ya Magantu kan Fasa Bututun Mai a Ribas, Ya Fadi Gaskiyar me ke Faruwa
- Rahotanni na nuni da cewa gwamnan Ribasa da aka dakatar ya musanta labaran da ake yadawa kan fashewar bututun mai a jihar
- Gwamna Siminalayi Fubara ya nesanta kansa daga kowacce kungiya ta 'yan bindiga ko masu tayar da zaune tsaye a Ribas
- Bayan haka, Simi Fubara ya gargadi masu yada labaran karya a shafukan sada zumunta da su daina haddasa rudani a jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Gwamnatin Ribas ta nesanta kanta daga wasu hotuna da bidiyoyi da ke yawo a shafukan sada zumunta, inda ake ikirarin an fasa bututun mai a wasu sassan jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu gurbatattun mutane na kokarin alakanta wadannan bidiyoyi da magoya bayan gwamna Siminalayi Fubara.

Asali: Facebook
Babban sakataren yada labaran gwamnan, Nelson Chukwudi ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a Facebook, cewa ba a fasa bututun mai ba wuraren da ake zargi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, al’ummomin da ake ikirarin cewa an fasa bututun mai a yankunansu sun fito fili sun karyata labarin.
Nelson Chukwudi ya tabbatar da cewa dukkanin kayayyakin gwamnati da ke yankunan suna nan cikin aminci da kariya.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Siminalayi Fubara ba zai lamunci yunkurin tayar da zaune tsaye ba, yana mai gargadin masu yada irin wadannan labarai marasa tushe.
Fubara ya nesanta kansa daga 'yan ta'adda
Gwamna Siminalayi Fubara ya nesanta kansa daga kowacce kungiya ta 'yan bindiga ko masu tayar da fitina a jihar Ribas ko yankin Niger Delta.
Ya bayyana cewa ba zai taba mara wa kowanne dan ta'adda baya ba, kuma yana da burin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Fubara ya nanata cewa zaman lafiya shi ne ginshikin ci gaba, don haka zai ci gaba da kokarin ganin an samu kwanciyar hankali a Ribas.
Ya kara da cewa yana da kwarin gwiwa cewa muddin aka samu zaman lafiya, to za a iya aiwatar da shirye-shiryen ci gaba da kuma samar da ayyukan yi ga jama'a.
Fubara ya gargadi masu yada labaran bogi
Fubara ya gargadi masu yada labaran karya a shafukan sada zumunta da su daina tayar da hankalin jama'a da rahotannin bogi.
Ya bayyana cewa labaran bogi na haifar da matsaloli da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban jihar.
Vanguard ta wallafa cewa ya bukaci hukumomin tsaro su dauki matakin da ya dace domin gano masu yada wadannan bidiyoyi tare da gurfanar da su a gaban shari'a.
A cewarsa, irin wadannan rahotannin bogi sun haddasa rudani a kwanakin baya, wanda hakan ke iya jefa jihar cikin mawuyacin hali.

Asali: Facebook
Sabaoda sabanin siyasa da aka samu a jihar ne Bola Tinubu ya dakatar da Simi Fubara tare da nada shugaban riko a jihar.
An fara maganar sulhun rikicin Rivers
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnoni a yankin Kudu maso Kudu sun fara maganar sulhu domin daidaita lamuran siyasa a jihar Ribas bayan dakatar da gwamna.
Bangaren ministan Abuja, Nyesom Wike sun nuna gamsuwa da daukar matakin sulhu kan rikicin da ya jawo dakatar da gwamna Simi Fubara da 'yan majalisar jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng