Fubara: Gwamnonin PDP Sun Nufi Kotun Koli kan Dokar Ta Baci a Jihar Ribas

Fubara: Gwamnonin PDP Sun Nufi Kotun Koli kan Dokar Ta Baci a Jihar Ribas

  • Da alama gwamnonin PDP ba za su nade hannayensu a kan dokar ta-ɓaci da Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana a jihar Ribas ba
  • Za a iya tuna cewa Shugaban kasar nan ya dakatar da gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, da 'yan majalisar dokokin Ribas
  • An gano cewa gwamnonin sun haɗe kai wajen ɗaukar matakin da suke sa ran zai dawo da gwamnan Ribas domin ya ci gaba da mulki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnonin jam’iyyar PDP sun umarci lauyoyinsu da su shigar da ƙara a kotu domin ƙalubalantar ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas da Shugaban Kasa ya yi.

An shirya shigar da ƙarar a kotun koli a cikin wannan mako, inda Majalisar ƙasa za ta kasance a matsayin mai kare ƙara na biyu.

Kara karanta wannan

Nasarori 3 da Nyesom Wike ya samu a cikin kwanaki 3 a siyasar jam'iyyar PDP

Adawa
Gwamnonin PDP Hoto: PDP Governors' Forum
Asali: Facebook

A rahoton da ya kebanta ga jaridar The Cable, an bayyana cewa gwamnonin PDP daga jihohin Bauchi, Adamawa, Bayelsa, Enugu, Osun, Filato da Zamfara ne za su jagoranci shigar da ƙarar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar 18 ga watan Maris ne Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas, yana mai cewa hakan ya zama dole sakamakon rikicin siyasa da lalata kayayyakin mai a jihar.

Gwamnonin PDP na son kotu ta soke dokar ta-ɓaci

A taron gwamnonin PDP da aka gudanar ta yanar gizo a ranar Laraba, sun sha alwashin daukar matakin ƙalubalantar dokar ta-ɓacin da aka ayyana a jihar Ribas.

Dangane da hukunci da kotun koli ta riga ta yanke a baya, Gwamna Siminalayi Fubara ba zai iya shiga cikin ƙarar ba saboda yana bukatar sahalewar shugabancin jihar kafin ya iya haka.

Gwamnoni
Gwamnonin PDP za su kai Tinubu kotu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A karar da ake shirin shigar wa, gwamnonin PDP na roƙon kotu ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ba shi da ikon dakatar da gwamnati da aka zaɓa ta hanyar dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Yadda Akpabio ya "murkushe" yan majalisa da suka ki amincewa da dokar ta-baci

Sun gina hujjarsu ne kan sashe na 1(2), 5(2), da 305 na kundin tsarin mulki, wanda ke cewa:

“Shugaban Tarayyar Najeriya ba shi da wani iko ko hurumin dakatar da gwamna da mataimakinsa da aka zaɓa ta hanyar dimokuradiyya a kowace jiha a Najeriya."

“A dawo da gwamnan Ribas,” Gwamnonin PDP

Masu shigar da ƙarar za su bukaci kotun koli ta ayyana dakatar da gwamna Fubara, mataimakinsa da 'yan majalisar dokokin Ribas a matsayin haramun kuma saba doka.

Gwamnonin na PDP na ƙalubalantar naɗin mai mulkin rikon kwarya a jihar, suna masu cewa Shugaban kasa ba shi da ikon yin irin wannan naɗi bisa kundin tsarin mulkin ƙasa.

Saboda haka, suna roƙon kotu da ta soke naɗin tsohon babban jami'in sojin ruwan kasar nan, Ibok-Ete Ibas a matsayin mai mulkin rikon kwarya na jihar Ribas.

Sun jaddada cewa sanarwar dokar ta-ɓaci ba ta bi ƙa’idojin da doka ta tanada ba, kuma an yi ta ne bisa wasu dalilai da ba su dace da tanadin kundin tsarin mulki ba.

Kara karanta wannan

Dokar ta baci a Ribas: Ana zargin Shugaba Tinubu da 'juyin mulki'

Tinubu zai janye dokar ta-ɓaci a Ribas

A baya, kun ji cewa Ministan yaɗa labarai da wayar da kai, Mohammed Idris, yce Shugaba Bola Tinubu zai janye dokar ta-ɓaci da aka kakaba a jihar Ribas da zarar an samu daidaito.

Ministan ya tabbatar da cewa Shugaban kasar na da niyyar ganin cewa Ribas ta koma cikakken mulkin dimokuraɗiyya cikin gaggawa, kuma ba shi da niyyar kakaba wa jihar gwamna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng