Ana Jimamin Mutuwar Mahaifiyar Gwamna, Kakakin Ƴan Sanda Ya Rasu
- Kakakin rundunar ‘yan sandan Taraba, Abdullahi Usman, ya rasu a safiyar Lahadi, lamarin da ya girgiza hukumomi da al’ummar jihar
- Mataimakin PPRO, Gambo Kwache, ya tabbatar da mutuwarsa, yayin da aka bayyana cewa Abdullahi Usman ya rasu a kan hanyar asibitin FMC
- Rahotanni sun bayyana cewa za a gudanar da jana’izar kakakin 'yan sandan da misalin karfe 2:00 na rana a makabartar ‘yan sanda ta Jalingo
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Taraba - Kakaki kuma jami'in hulda da jama'a na rundunar ‘yan sanda a jihar Taraba, Abdullahi Usman, ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da rashin lafiya.
Wannan na zuwa ne, yayin da 'yan Najeriya, musamman Katsinawa, ke jimamin mutuwar mahaifiyar Gwamna Dikko Radda, wadda aka yi wa sutura a ranar Lahadi.

Source: Twitter
Kakakin 'yan sandan jihar Taraba ya rasu
Mataimakin PPRO, Gambo Kwache, wanda ya rike mukamin kakakin wucin gadi a lokacin da Usman ke jinya, ya tabbatar da mutuwarsa ga jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce Abdullahi Usman, wanda ya shafe shekaru uku a matsayin kakakin rundunar, ya rasu a safiyar Lahadi a gidansa da ke Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Gambo Kwache ya ce ya farka daga barci ya ga kira 14 da sakon mutuwar Usman, inda ya ce zai je wurin kafin ya yi karin bayani.
"Ina barci lokacin da ya rasu. Da na farka, na ga kira 14 a wayata da sakon da ke cewa 'Oga ya rasu'. Zan kira ka; bari na fara isa wurin tukunna," in ji Kwache.
Kakakin 'yan sandan ya rasu da asubah
Haka nan, abokin marigayin, Ahmed Manga, ya tabbatar da rasuwar Usman yayin da yake magana da wakilinmu ta wayarsa.
Manga ya bayyana cewa Usman ya rasu da misalin karfe 5:00 na Asubahin ranar Lahadi bayan rashin lafiya ta turnuke shi a daren ranar.
A cewarsa, sun yi yunkurin kai shi asibitin tarayya na Taraba (FMC Jalingo), amma ya rasu kafin su isa can.

Kara karanta wannan
Ramadan: Dan Majalisa Kirista ya yi wa Musulmi bazata bayan bukatar babban limami
Bayan isarsu asibitin, likitoci sun tabbatar da mutuwar Abdullahi Usman, lamarin da ya girgiza rundunar ‘yan sanda da abokansa da ke jihar.
An sanya lokacin jana'izar kakakin 'yan sandan

Source: Original
Jaridar The Sun ta rahoto Ahmed Manga ya na cewa:
"Ya yi fama da rashin lafiya, duk da cewa ba mai tsanani ba ce, sai a daren jiya ne jikin nasa ya yi tsanani sosai. Mun dauke shi domin kai shi Asibitin Tarayya (FMC) Jalingo.
"Amma kafin mu isa, ya rasu a hanya. Bayan mun isa asibitin ne likitoci suka tabbatar da rasuwarsa."
An shirya jana’izarsa da misalin karfe 2 na rana a makabartar ‘yan sandan Taraba da ke Jalingo, bisa tsarin addinin Musulunci.
Tinubu ya kadu da rasuwar mahaifiyar gwamna
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaba Bola Tinubu ya aikawa gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda sakon ta'aziyya bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari.
Marigayiyar, mai shekaru 93, ta rasu a daren ranar Asabar, 23 ga watan Maris 2025, a wani asibiti da ke babban birnin tarayya, Abuja.
Tinubu ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin mace ta-gari wadda ta reni shugabanni da dama da suka yi fice a fannoni daban-daban na kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
