Minista Ya Fadi Lokacin da Tinubu zai Janye Dokar ta Baci a Ribas
- Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya kare shugaba Bola Tinubu kan sanya dokar ta-ɓaci a ihar Ribas
- Ministan ya ce al’amuran shugabanci da dimokuraɗiyya sun lalace a jihar, lamarin da ya tilasta wa Tinubu dakatar da gwamnan Ribas
- Ya ce Shugaban Ƙasa ba shi da niyyar karɓe iko da jihar ko kakaba mata gwamna, kuma za a janye dokar idan al’amura sun daidaita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai janye dokar ta ɓaci da aka kakaba a Ribas da zarar an samu daidaito da kwanciyar hankali.
Ministan ya tabbatar da cewa Tinubu na da niyyar tabbatar da cewa Ribas ta koma cikakken mulkin dimokuraɗiyya da wuri-wuri kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan
Ribas: Tambuwal ya tona yadda aka yi watsi da doka a majalisa don biyan buƙatar Tinubu

Asali: Facebook
A wata hira da ya yi da The Nation, Ministan ya bayyana cewa, da zarar shugaba Tinubu ya ga an samu daidaito a Ribas, zai tabbatar da mayar da dukkanin tsarin dimokuraɗiyya a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Minista ya fadi manufar Tinubu kan Ribas
Mohammed Idris ya jaddada cewa shugaba Tinubu ba shi da wani niyya na karɓar mulkin Ribas ko naɗa gwamna a jihar kamar yadda ake hasashe.
Ya nanata cewa:
"Shugaban ƙasa ba shi da wani shiri ko nufin ɗaukar ragamar mulkin Ribas. Ba shi da niyyar zama gwamna ko naɗa wani a matsayin gwamna a jihar."
Ministan ya kare matakin da Shugaban ƙasa ya ɗauka, yana bayyana shi a matsayin mataki mai matukar ciwo, amma ya zama dole, wanda aka yi bisa tanadin kundin tsarin mulki.
"An samu matsala a Ribas." – Ministan labarai
A cewar Mohammed Idris, tsarin mulki da harkokin mulki sun rushe gaba ɗaya a jihar Ribas, inda majalisar dokoki ta daina aiki kuma sashen zartarwa ke fuskantar matsaloli masu tsanani.

Kara karanta wannan
Rikicin Ribas: An ƙara samun bayanai kan dalilin shugaba Tinubu na dakatar da gwamna

Asali: Twitter
Ya ƙara da cewa:
"Dimokuraɗiyya a ƙasar nan an tsara ta ne a kan ginshiƙan rassan gwamnati guda uku – zartarwa, shari’a da dokoki – waɗanda ke kula da juna.
Ba za a ce muna da cikakkiyar dimokuraɗiyya ba idan sashen zartarwa kaɗai ke aiki, shi ya sa Shugaban ƙasa ya ɗauki mataki don hana jihar yin tafiya zuwa rikici da rashin doka da oda."
Ministan ya ce tsarin mulkin Najeriya ya riga ya tanadi irin wannan yanayi, wanda ya sa Shugaban ƙasa ya dogara da dokar ƙasa wajen amfani da ikonsa domin ɗaukar matakin da ya dace.
An zargi Tinubu da juyin mulki a Ribas
A wani labarin, kun ji cewa babban lauya kuma masanin kundin tsarin mulkin Najeriya, Mike Ozekhome (SAN), ya yi suka kan ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas da Bola Tinubu ya yi.
Ozekhome ya ce dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar ba bisa ka’ida ba ne, kuma daidai ya ke da juyin mulkin farar hula.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng