Dokar Ta Baci: Bayan Rivers, An Fadawa Tinubu Gwamnan da Ya Kamata Ya Dakatar
- Tsohon ministan harkokin ‘yan sanda, Oyewale Adesiyan, ya bukaci a ayyana dokar ta-baci a Osun saboda tabarbarewar tsaro da rikicin siyasa
- Ya zargi Gwamna Ademola Adeleke da kin bin umarnin kotu, yana mai cewa hakan ne ya haddasa rikicin kananan hukumomi da asarar rayuka
- Adesiyan ya bukaci a yi amfani da Sashe na 305 na kundin tsarin mulki don tabbatar da doka da oda tare da dawo da zaman lafiya a Osun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - Tsohon ministan harkokin ‘yan sanda, Oyewale Adesiyan, ya bukaci a ayyana dokar ta-baci a jihar Osun saboda tabarbarewar tsaro da rikicin siyasa.
Adesiyan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a Osogbo ranar Lahadi, yana mai dogaro da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan
Ramadan: Dan Majalisa Kirista ya yi wa Musulmi bazata bayan bukatar babban limami

Asali: Twitter
Dalilan neman ayyana dokar ta baci a Osun
A cewarsa, Osun na fuskantar barazana, tun daga rikicin kananan hukumomi zuwa kin bin umarnin kotun daukaka kara daga bangaren gwamnan jihar, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya zargi Gwamna Ademola Adeleke da nuna rashin biyayya ga hukuncin kotu, wanda ya ce hakan ne ya haddasa rikicin da ya kai ga salwantar rayukan mutane.
Adesiyan ya ce rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, ciki har da shugaban karamar hukumar Irewole, Hon. Remi Abass.
Osun: Tsohon minista ya fadi matsalolin gwamna
Tsohon ministan ya bayyana cewa, rashin iya tafiyar da mulki daga bangaren gwamnan ne ya haddasa tabarbarewar siyasa da rashin tsaro a jihar.
"Tare da rikice-rikicen siyasa a jihar Osun da kuma samun gwamna maras kwarewa wajen shawo kan lamarin a wannan jiha, ina ganin ya fi dacewa a yi amfani da kundin tsarin mulki da ya dace domin dawo da zaman lafiya a Osun."
- Oyewale Adesiyan.
Ya nuna damuwa kan yadda aka rasa rayuka yayin rikicin kananan hukumomi, yana mai cewa rikicin kabilanci na baya-bayan nan ya tilasta wa mutane da dama barin gidajensu.
Ya tambaya ko kafin rikicin, ba a samu rahoton tsaro a teburin gwamna da ke nuna yiyuwar tashin hankali ba?
Tsohon minista ya nemi ayyana dokar ta baci a Osun

Asali: Twitter
Adesiyan ya caccaki matakin da Gwamna Adeleke ya dauka na sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 bayan an riga an yi asarar rayuka da dukiyoyi.
Ya ce irin wannan gazawar jagoranci ce ke haifar da matsaloli, yana mai kwatanta abin da ya faru a Osun da rikicin da ya janyo dokar ta-baci a Rivers.
Tsohon ministan ya gode wa Shugaban Kasa Bola Tinubu bisa matakin da ya dauka a Rivers, yana mai cewa da ba ayi hakan ba, to da lamarin ya munana.
Ya jaddada cewa ya dace a yi amfani da sashe na 305 na kundin tsarin mulki don tabbatar da doka da oda a jihar Osun.
Mafitar da ake nema
Adesiyan ya ci gaba da jaddada cewa rikicin siyasa da tabarbarewar tsaro a Osun na bukatar daukar matakin gaggawa domin gujewa kara dagulewa.
Ya ce rashin biyayya ga umarnin kotu da Gwamna Adeleke ke yi na kara rura wutar rikici, yana mai gargadi cewa hakan na iya jefa jihar cikin yanayi mafi muni.
A cewarsa, ‘yan bindiga da ‘yan daba na cin karensu babu babbaka a wasu sassan Osun, lamarin da ke hana jama’a walwala.
Ya ce idan har ba a dauki mataki cikin gaggawa ba, za a iya fuskantar rikici mai kamari fiye da wanda ya addabi jihar Kano ko Rivers.
Matsayar majalisar jiha
A bangaren ‘yan majalisar dokokin jihar, wasu daga cikinsu sun bukaci gwamnatin tarayya da kada ta yi gaggawar ayyana dokar ta-baci, inda suka bukaci Adeleke da ya dauki kwararan matakai don magance matsalolin tsaro da rikicin kananan hukumomi.
A halin da ake ciki, wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a Osun sun goyi bayan bukatar Adesiyan, suna masu cewa dokar ta-baci ita ce mafita ga halin da ake ciki.
Duk da haka, wasu daga bangaren PDP sun yi watsi da bukatar, suna masu cewa Osun na cikin kwanciyar hankali fiye da yadda ake zato.
Fubara ya magantu bayan dakatar da shi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Siminalayi Fubara ya musanta zargin Bola Tinubu cewa ya rusa majalisar dokokin Rivers ba tare da sake gina ta ba.
Ya bayyana cewa ya dauki matakan kare albarkatun man jihar, kuma sabuwar majalisar dokoki ta kusa kammaluwa da kashi 80%.
Fubara ya zargi Ministan Abuja, Nyesom Wike, da haddasa rikici a jihar ta hanyar furta kalaman da suka tayar da hankalin ‘yan kabilar Ijaw.
Asali: Legit.ng