Ramadan 2025: Ana Tafka Tsananin Zafin Rana a Kano, Masu Azumi Sun Koma Shan ORS
- A Kano, jama’a na amfani da gishirin ORS don rage gajiya da samun kuzari yayin azumi, saboda tsananin zafin rana da ya kai mizanin 40°C
- Masu sayar da magunguna sun tabbatar da karancin ORS saboda yawan sayensa da ake yi, yayin da direbobi suka kauracewa Fearless suka koma ORS
- Likitoci sun gargadi mutane da su guji shan ORS ba tare da sahalewar likita ba, suna mai cewa ruwa da ‘ya’yan itatuwa sun fi dacewa ga masu azumi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - A yayin da zafin rana ke karuwa a jihar Kano a cikin wannan watan Ramadan, jama’a na amfani da gishirin ORS don hana kasala da kuma rage jin kishin ruwa yayin azumi.
Zazzafar rana da ke kaiwa sama da 40°C ya janyo karuwar bukatar ORS, inda masu sayar da maganin ke fuskantar karancinsa saboda yawan saye da ake yi.

Asali: Getty Images
Jama’a na tururuwar siyan ORS
A cewar wakilin Legit.ng, Usman Bello Balarabe, wasu shagunan magani a Kano sun fara rasa ORS saboda yawan saye da ake yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malam Ahmed Musa, mai sayar da magunguna a kasuwar Dangwauro, ya tabbatar da haka, yana mai cewa:
"A bana, bukatar ORS ya yi matukar tashi. Mutane da dama na saye don hana su saurin gajiya yayin azumi, domin ana tsananin zafin rana a bana."
ORS dai wani sinadari ne da ke hade da gishiri da sukari, wanda ake narkarwa a ruwa, kuma ana amfani da shi wajen rage matsalar rashin ruwa a jiki saboda gudawa ko zufa mai yawa.
ORS ya zama mafita ga masu azumi
A wannan azumin na Ramadan, ORS ya zama babbar mafita ga jama’a da ke fama da tsananin zafin rana mai tsanani a Kano.
Hajiya Fatima Usman, wata mata mai yara hudu, ta shaidawa wakilunmu cewa:

Kara karanta wannan
Wuri ya yi wuri: An daka wawar kayan abinci a motar Majalisar Dinkin Duniya a Borno
"Muna amfani da ORS don mu samu ƙarfi yayin azumi. Saboda zafin rana, muna amfani da shi don taimakawa jikinmu samun kuzari da gujewa saurin kasala da gajiya."
Sani Ibrahim, direban adaidaita sahu, ya ce yana shan ORS bayan buda baki:
"Yana sa in murmure da sauri kuma in shirya don tunkarar azumin washegari. A baya, ina amfani da lemun karin karfi na Fearless, amma an ce min ORS yafi amfani."
Likitoi sun yi gargadi kan amfani da ORS

Asali: Getty Images
Duk da haka, Dr Abdullahi Kabir Suleiman, kwararre a asibitin koyarwa na Aminu Kano, ya gargadi jama’a da su guji shan ORS ba tare da shawarar likita ba.
"ORS magani ne da ake amfani da shi don rage rashin ruwa ga masu gudawa. Amma yana dauke da wasu abubuwa da ka iya haifar da matsala ga wasu mutane," in ji shi.
Ya kara da cewa:
"A mafi yawan lokuta, ruwa ko abinci mai dauke da ruwa kamar 'ya'yan itatuwa yafi. Saboda haka, a guji shan ORS haka kawai ba da wani kwakkwaran dalili ba."
Shi ma Dr. Shamsudeen Mohammed, daga asibitin Katsina, ya ce yawan shan ORS ba tare da jiki na bukatar hakan ba na iya haifar da matsaloli saboda yawan gishiri da sinadaran 'electrolytes' a jiki.
Dr. Shamsudeen ya ce:
"Shan ORS mai yawa na iya haifar da matsalar 'hyperkalemia' ko 'hypokalemia', wato karanci ko yawan sinadarin 'potassium' a jiki. Wannan na iya sanya zuciya ta rika bugawa ba bisa ka'ida ba, yana sa raunin tsokoki, kasala, da ciwon ciki."
Ya ce a maimakon mutane su rika amfani da ORS saboda gudun shan wahala a lokacin azumi, zai fi dacewa su rika shan ruwa mai yawa da ruwan ‘ya’yan itatuwa, wanda ke hana saurin tsotsewar ruwan jiki.
'Azumi a zafin rana na da dumbin lada' - Rijiyar Lemo
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sheikh Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo ya ce yin azumi a yanayi na zafin rana, yana dauke da dumbin lada ga duk wanda ya tsarkake niyyarsa.
Fitaccen malamin addinin ya jaddada cewa, duk wata wahala da za ta samu mutum a dalilin biyayya ga Allah, to za a rubuta masa lada a kai, a kuma daga darajarsa.
Asali: Legit.ng