Bayan Sace Ɗaliban Jami'a, Ƴan Bindiga Sun Sake Komawa Katsina, Sun Kashe Mutane

Bayan Sace Ɗaliban Jami'a, Ƴan Bindiga Sun Sake Komawa Katsina, Sun Kashe Mutane

  • 'Yan bindiga sun kai hari a kauyen Taka Lafiya da ke karamar hukumar Batsari, jihar Katsina, inda suka kashe wasu mutane biyu
  • Maharan sun afka kauyen da misalin karfe 4:30 na ranar Asabar, dauke da bindigogi kirar AK-47, suna harbe-harbe kan mai uwa da wabi
  • Bayan an garzaya da wadanda aka harba, Abdulmajid Takalafiya da Sahalu Dayyabu zuwa asibiti, likitoci suka tabbatar da mutuwarsu
  • Wannan harin na Taka Lafiya, na zuwa ne bayan sace wasu daliban jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma, inda har yanzu ake kokarin ceto su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - 'Yan bindiga dauke da mugayen makamai sun sake kai hari jihar Katsina, 'yan kwanaki kadan bayan sace daliban jami'ar FUDMA.

Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan bindigar, a wannan karon, sun farmaki kauyen Taka Lafiya da ke wajen karamar hukumar Batsari.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun je har gida, sun kashe shugaban Miyetti Allah ana cikin Azumi

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe mutane 2 a harin da suka kai Katsina
'Yan bindiga sun kai sabon hari jihar Katsina tare da kashe mutane 2. Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

'Yan bindiga sun kai hari kauyen Katsina

Zagazola Makama, mai shari kan harkokin tsaro a yankin Arewa maso Gabas da Tafkin Chadi, ya fitar da wannan rahoton a shafinsa na X a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton Makama ya nuna cewa maharan, sun kashe mutane biyu ta hanyar bude masu wuta da bindiga, lamarin da ya jefa al'ummar garin cikin tashin hankali.

An ce, 'yan bindigar sun kai harin da misalin karfe 4:30 na ranar Asabar, dauke da bindigogi kirar AK-47, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi.

Likitoci sun tabbatar da mutuwar mutane 2

A yayin da suka bude wuta, an ce harsashin bindiga ya samu wani Abdulmajid Takalafiya da Sahalu Dayyabu, inda aka garzaya da su asibiti bayan tafiyar 'yan bindigar.

Sai dai, rahoton ya ce, likitoci a babban asibitin Batsari, sun tabbatar da mutuwar Abdulmajid da Sahalu, sakamakon mummunan raunin harbin bindiga.

Kara karanta wannan

Wuri ya yi wuri: An daka wawar kayan abinci a motar Majalisar Dinkin Duniya a Borno

A halin yanzu dai, an ce asibitin ya mika gawar wadannan mutane biyu ga iyalansu domin a yi masu sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

'Yan bindiga sun sace daliban jami'ar FUDMA

Kamar yadda muka bayyana, harin 'yan bindiga na Taka Lafiya na zuwa ne 'yan kwanaki kadan bayan da wasu 'yan bindigar suka sace daliban jami'ar tarayya ta Dutsinma, jihar Katsina.

Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina
Gwamnan Katsina, Dikko Radda a ranar da ya kaddamar da rundunar tsaro ta jihar. Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Mahara sun kai farmaki a unguwar Graveyard Quarters da ke kan titin Tsaskiya a garin Dutsin-Ma da misalin karfe 2:40 na tsakar dare, inda suka sace wasu dalibai.

Wata majiya ta bayyana cewa bayan samun kiran gaggawa, jami’an tsaro sun garzaya domin dakile harin da kuma kokarin ceto mutanen da aka sace.

Duk da haka, rahoton Legit.ng Hausa ya nuna cewa maharan sun tsere kafin jami’an tsaro su samu nasarar dakatar da su.

An ce hukumar tsaro ta tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike da kokarin ganin an kubutar da daliban.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Katsina da 'yan bindiga suka sace wasu ɗaliban jami'a

Duba rahoton harin garin Taka Lafiya a nan kasa:

'Yan bindiga sun kashe sojojin Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai hare-hare a garuruwa biyu da ke ƙaramar hukumar Kwande, Jihar Benue, inda suka kashe mutum biyar, ciki har da sojoji biyu.

Gwamnatin jihar ta yi Allah-wadai da harin tare da nuna alhini kan mutuwar waɗanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan farmaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.