Duniya ba Tabbas: Mahaifiyar Gwamna Dikko Radda Ta Rasu Ana Azumin Ramadan
- An shiga jimami a jihar Katsina sakamakon rasuwar Hajiya Safara’u Umar Radda, mahaifiyar Gwamna Dikko Radda, a ranar Lahadi 23 ga Maris, 2025
- Hajiya Safara’u ta rasu bayan ta sha fama da doguwar jinya kamar yadda hadimin gwamna, Isah Miqdad, ya sanar a shafin X
- Sanarwar ba ta fadi lokacin jana'izarta ba, sai dai an bayyana cewa marigayiyar ta yi fama da jinya kafin rasuwarta
- Miqdad ya roki Allah ya jikan marigayiyar, tare da yi mata addu'ar rahama da samun gafara kamar yadda sanarwar ta bayyana
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Jihar Katsina ta shiga alhini bayan sanar da rasuwar mahaifiyar Gwamna Dikko Umaru Radda.
An sanar da rasuwar Hajiya Safara’u Umar Radda a yau Lahadi 23 ga watan Maris, 2025 bayan ta sha fama da jinya.

Kara karanta wannan
Tafsirin Ramadan ya tsaya, fitaccen malamin Musulunci ya rasa mahaifiyarsa a Borno

Asali: Twitter
Gwamna Dikko Umaru Radda ya yi rashi
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan a bangaren sadarwa ta zamani, Isah Miqdad ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, Miqdad ya ce dattijuwar ta rasu bayan tasha da fama da jinya mai tsawo.
Sai dai a cikin sanarwar bai bayyana lokacin da za a yi sallar jana'izarta ba da kuma sauran bayanai.
Daga bisani, ya yi mata addu'ar samun rahama daga Ubangiji tare da fatan Allah ya jikanta da sauran wadanda suka riga mu gidan gaskiya.
Sanarwar ta ce:
"Ina mai bakin cikin sanar da rasuwar Hajiya Safara’u Umar Radda, mahaifiyar Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, bayan fama da doguwar jinya. Allah ya jikanta, Amin."

Asali: Twitter
An jero fitattun ƴaƴan marigayiyar
Wani na kusa da dangin marigayiyar ya tabbatar da cewa ta rasu da safiyar Lahadi 23 ga watan Maris, 2025 bayan gajeriyar rashin lafiya.

Kara karanta wannan
Duniyar fina finan Najeriya ta yi rashi, fitacciyar jaruma ta rasu bayan mata tiyata
Har ila yau, wani da ke da kusanci da iyalin da ya tattauna da wakilin PM News ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin jigo kuma ginshikin iyalansu.
Ya ce marigayiyar ta kasance uwa ga kowa wacce take tausayawa na kasa da ita yayin da ya ce tabbas za a yi rashinta matuka.
Ya ce:
"Ta gudanar da rayuwarta cikin kaskantar da kai da kuma tausayi musamman ga dukan wadanda ke tare da ita.
Sauran fitattun ’ya’yan Hajiya Safara’u sun haɗa da Dagacin Radda, Alhaji Kabir Umar Radda, da Hajiya Hauwa Umar Radda, tsohuwar matar marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’adua.
Masu juyayi na ta tururuwa zuwa gidan don yi wa iyalanta ta’aziyya kan babban rashi da aka yi.
Mahaifiyar malamin Musulunci ta rasu a Borno
A jiya, mun ba ku labarin rasuwar mahaifiyar fitaccen malamin Musulunci a jihar Borno, Farfesa Sheikh Muhammad Alhaji Abubakar.
Malamin wanda shi ne babban limamin masallacin Indimi ya tsayar da gudanar da tafsirin Kur'ani na kwanaki biyu saboda rashin da aka yi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an gudanar da sallar jana'izar marigayiyar a jiya Asabar 22 ga Maris, 2025 a babban masallacin 505 da ke Maiduguri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng