Rivers: Abin da Shugaban Rikon Kwarya Ya Yi ga Ma’aikata bayan Shiga Ofis
- Shugaban rikon kwarya a Rivers, Ibok-Ete Ibas ya umarci a biya ma’aikatan kananan hukumomi albashinsu
- Ya ce an jinkirta biyan albashin ne sakamakon tsaikon kudi daga Abuja, wanda yanzu aka sako
- Ibas ya nemi rahoton albashi daga kananan hukumomi don tabbatar da gaskiya da tsafta a harkokin kudi
- Ya gargadi shugabanni da su guji almundahana, ya na mai cewa kobo daya ba za ta bace ba a karkashinsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Shugaban rikon kwarya a Rivers, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas ya fara da yi wa ma'aikata abin alheri a jihar.
Ibok-Ete Ibas wanda tsohon kwamandan rundunar sojin ruwa ne ya umarci a biya albashin ma’aikatan kananan hukumomi nan take.

Asali: Twitter
Ibas ya gana kungiyar NULGE a Rivers

Kara karanta wannan
Duniyar fina finan Najeriya ta yi rashi, fitacciyar jaruma ta rasu bayan mata tiyata
Ibas ya fadi haka ne a wani taro da ya gudanar da shugabannin gudanarwa na kananan hukumomi da kungiyar ma’aikata ta NULGE reshen jihar, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon hafsan sojojin ruwa a Najeriya ya bayyana takaicinsa kan yadda aka daina biyan albashin ma'aikata a jihar.
Ya ce:
“Jinkirin biyan albashin ma’aikata na watan Faburairu da Maris abin takaici ne, amma an jinkirta hakan ne saboda tsaikon kudi daga Abuja.
“Ina matukar jin zafin halin da ma’aikata ke ciki, don haka na bayar da umarni cewa a dauki mataki nan take.”

Asali: Twitter
Gargadin Ibas ga ciyamomi a jihar Rivers
Kotun Koli ce ta hana fitar da kudin da suka kamata jihar ta karba, amma yanzu an sako kudin, kuma Ibas ya ce ya fahimci wahalar da ma’aikata ke ciki.
Ibok-Ete Ibas ya ce kananan hukumomi na da muhimmiyar rawa a taimaka wa al’umma, kuma dole ne a gudanar da su da gaskiya da kulawa.
Ya kara da cewa:
“Mu shugabanni dole ne mu ji zafin da jama’a ke ciki, wannan ne tsarin shugabanci mai ma’ana da nake so mu bi.
Ya bukaci a gabatar masa da bayanan biyan albashi daga kowace karamar hukuma ta hannun ofishin shugaban ma’aikata, domin tabbatar da sahihanci.
Ibas ya gargadi shugabannin kananan hukumomi da su guji almubazzaranci, yana mai cewa zai tabbatar da gaskiya da kula da kowane kobo.
“Ko da ina da watanni shida kacal, zan tabbatar da cewa an san yadda kowace kobo ta fita a jihar Rivers.”
- Cewar Vice Admiral Ibas
Halin da ma'aikata ke ciki a Rivers
Shugaban NULGE na jihar, Clifford Paul, ya tabbatar da cewa ba a biya ma’aikata albashi ba na tsawon watanni biyu.
Ya ce rikicin siyasa ya dakile ci gaban jihar, amma ya nuna fata cewa zaman lafiya zai dawo da mulkin mai rikon kwarya.
Clifford ya bayyana goyon bayan ma’aikata ga kokarin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
An fadi halin da Fubara ke ciki
Mun ba ku labarin cewa wasu su na da yada labarin karya cewa dakataccen gwamnan Siminalayi Fubara yana cikin wani hali.
Sai dai kakakin Siminalayi Fubara da aka dakatar, Nelson Chukwudi, ya tabbatar da gwamnan ya na lafiya kuma babu matsala da lafiyarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng