Daga Fara Mulki, Shugaban Rikon Ribas Ya Yi Zazzafan Gargadi wa Sarakuna
- Ibok-Ete Ibas ya bukaci sarakunan gargajiya na Ribas da su guji siyasar bangaranci kuma su maida hankali kan tsaro
- Tsohon sojan ruwan ya ce jihar na da muhimmanci sosai ga ci gaban kasa, don haka dole ne a tabbatar da zaman lafiya a cikinta
- Shugaban majalisar sarakunan Ribas, Mai martaba Chike Worlu-Wodo, ya tabbatar da cewa za su mara wa Ibok-Ete Ibas baya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ribas - Shugaban riko na jihar Ribas, Ibok-Ete Ibas ya gargadi sarakunan gargajiya da su nisanci siyasar bangaranci tare da maida hankali kan samar da tsaro a yankunansu.
Shugaban rikon ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da sarakunan jihar a fadar gwamnati da ke Fatakwal.

Asali: Facebook
A cewar jaridar Vanguard, Ibas ya bukaci sarakunan da su taka rawar gani wajen tabbatar da doka da oda domin samun ci gaba mai dorewa a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon hafsan rundunar sojan ruwan ya ce ya na da matukar damuwa kan rikice-rikicen da ke addabar jihar Ribas.
An rahoto shi ya ce yana da burin dawo da jihar bisa turbar zaman lafiya da ci gaba.
Ibas ya bukaci sarakuna su tabbatar da tsaro
A yayin ganawar da sarakunan, Ibas ya bayyana cewa yana son ganin jihar Ribas ta zama wuri mai kwanciyar hankali. Ya ce yana da ra’ayi mai karfi kan ci gaban yankin Neja Delta gaba daya.
A cewarsa, matsalolin rashin zaman lafiya da tashe-tashen hankula suna hana jihar samun ci gaba.
A cewarsa:
“A matsayina na tsohon hafsan sojan ruwa, babban aikina shi ne kare rayuka. Kuma zan ci gaba da kokari wajen dawo da zaman lafiya a jihar Ribas,”
Gargadin sarakunan Ribas kan siyasar bangaranci
Ibas ya jaddada cewa babu wata al’umma da za ta samu ci gaba idan babu doka da oda. Ya bukaci sarakunan da su kauce wa duk wani abu da zai nuna suna da bangaranci a siyasa.
Ya tunatar da su cewa nauyin samar da tsaro ya rataya ne a wuyan kowa, ba kawai gwamnati ba. Ya ce gwamnatin sa ba za ta lamunci wani dalili na rashin doka da oda ba.
Sarakuna sun yi alkawarin mara wa Ibas baya
A nasa jawabin, shugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar Ribas, HRM Chike Worlu-Wodo, ya tabbatar wa da Ibas cewa za su goyi bayan kokarinsa na dawo da zaman lafiya a jihar.
Rahoton Channels TV ya nuna cewa ya ce sarakuna sun san cewa babban aikinsu shi ne tabbatar da zaman lafiya a yankunansu, kuma za su yi duk mai yiwuwa don ganin hakan ta tabbata.
An bukaci Ibas da ya yi aiki a matsayin mai sulhu
Sarakunan sun bukaci Ibas da ya dauki kansa a matsayin mai sulhu a jihar Ribas, domin tabbatar da zaman lafiya da daidaito.
Sun ce Ribas na bukatar zaman lafiya fiye da komai, kuma suna da yakinin cewa zai yi nasara wajen wannan aiki da aka daura masa.

Asali: Facebook
Dakatar da Fubara: An maka Tinubu a kotu
A wani rahoton, kun ji cewa, matasan kabilar Ijaw sun maka shugaban kasa Bola Tinubu a kotun ECOWAS kan dakatar da gwamna Simi Fubara.
Matasan sun ce matakin da shugaban kasar ya dauka ya saba dokar kasa, a kan haka suka bukaci a ci tarar Bola Tinubu tarar Dala miliyan 10.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng