Baban Chinedu Ya Ajiye Barkwanci, Ya Fara Wa'azin Musulunci da Mukabala da Kiristoci

Baban Chinedu Ya Ajiye Barkwanci, Ya Fara Wa'azin Musulunci da Mukabala da Kiristoci

  • Malamin addini, Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah, ya jinjinawa Baban Chinedu kan fara wa’azi da kalubalantar Kiristoci
  • Sheikh Asadussunnah ya ce abin da Baban Chinedu yake yi kariya ce ga tauhidi, yana bukatar a goyi bayansa gaba daya
  • Malamin ya bukaci dan wasan barkwanci ya ci gaba da wa’azi, yana mai yaba masa kan shigar da yake yi yayin wa’azin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Fitaccen malamin addini, Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah, ya nuna jin dadinsa kan yadda shahararren dan wasan barkwanci na Kannywood, Baban Chinedu, ya rungumi wa’azi.

A cewar malamin, ya zama dole a yaba wa mutanen da suke kokarin kare addini, domin hakan wata hanya ce da za a karfafa su.

Baban Chinedu
Sheikh Asadussunah ya yaba wa Baban Chinedu. Hoto: Sheikh Musa Yusuf Asadussunah|Baban Chinedu
Asali: Facebook

Malamin ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa a wani bidiyo da ya wallada a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

An ba kowane sanata $15,000 kafin su amince da dokar ta ɓaci a Ribas? Bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Asadussunnah ya ce duk wanda Allah ya sa a zuciyarsa ya yi irin wannan aiki, wajibi ne a tallafa masa.

Malamin ya ce duk wanda ya fahimci ma’anar tauhidi zai gane cewa abin da Baban Chinedu yake yi yana da matukar muhimmanci.

An yaba da wa’azin Baban Chinedu

Sheikh Asadussunnah ya bayyana cewa babu laifi a kan yadda Baban Chinedu ya fara wa’azi ko da kuwa ana masa ganin shi ba malami ba.

Ya ce babban abin farin ciki shi ne yadda Baban Chinedu yake yin wa’azi domin kare tauhidi da kuma ilmantar da mutane.

Malamin ya kara da cewa idan Allah ya tashi taimakon addini, yana yin hakan ta hanyoyi da dama, ciki har da wadanda ba a zato.

Ya ce abin da Baban Chinedu yake yi ba wasan kwaikwayo ba ne, kariya ce ga tauhidi da kuma yada gaskiya.

Kara karanta wannan

Yadda Sheikh Pantami ya kubuta daga sharrin 'yan fashi bayan harbi 3 a titi

Sheikh Asadussunnah ya bukaci ya cigaba

Baya ga yaba masa, Sheikh Asadussunnah ya bukaci Baban Chinedu da ya ci gaba da wa’azi da kuma kalubalantar mabiya addinin Kirista.

Sheikh Asadussunnah ya ce idan Kiristoci na ganin ba daidai ba ne, sai su fito su kawo hujjojinsu su kalubalance shi.

Har ila yau, malamin ya yaba da shigar da Baban Chinedu yake yi lokacin wa’azi, inda ya ce yin hakan na kara jan hankalin masu sauraro.

A karkashin haka ya bukace Baban Chinedu da ya ci gaba da sanya tabarau da rawani a lokacin wa’azinsa.

Mutane sun yi mamakin Baban Chinedu

Bidiyon da malamin ya wallafa ya dauki hankalin mutane da dama ganin cewa dan wasan barkwanci na Kannywood ya rungumi wa’azi.

Baban Chinedu
Baban Chinedu a shigar barkwaci. Hoto: Baban Chinedu
Asali: Facebook

Mutane da dama sun nuna jin dadinsu kan wannan mataki da Baban Chinedu ya dauka, inda suka bukaci ya ci gaba da wa’azi tare da kokarin fadakar da mutane da gaskiya.

Kara karanta wannan

Wuri ya yi wuri: An daka wawar kayan abinci a motar Majalisar Dinkin Duniya a Borno

Haduwar Sheikh Pantami da 'yan fashi

A wani rahoton, kun ji cewa, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya bayar da labarin yadda suka hadu da 'yan fashi a hanyar Maiduguri.

Sheikh Pantami ya ce daya daga cikin 'yan fashin ya kusa kashe shi, har ya yi harbin bindiga sau uku amma Allah ya kare shi saboda addu'ar da ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng