'Suna da Sarkinsu, Muna da Namu': An Fadi Lokacin da Aminu Ado Zai Yi Sallar Idi a Kano

'Suna da Sarkinsu, Muna da Namu': An Fadi Lokacin da Aminu Ado Zai Yi Sallar Idi a Kano

  • Tsohon kwamishina a Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso, ya ce Muhammadu Sanusi II Sarkin gwamnati ne, amma Aminu Ado Bayero Sarkin al’umma ne
  • Kwankwaso ya bayyana cewa mutane sun fi son Aminu Ado Bayero saboda amincewarsu da shi, yayin da gwamnati ta nada Sanusi a matsayin Sarki
  • Shahararren 'dan siyasar ya ce babu wata matsala, kowa yana da Sarki nasa, kuma Aminu Ado zai fito filin idi karfe 7:00 na safe ranar Sallah
  • Musa Kwankwaso ya bukaci jama'a su fita Sallah lafiya, ya kuma ce babu ruwansu da Sanusi ko wasu shirye-shiryen gwamnatin NNPP

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Tsohon kwamishina a Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi magana kan rigimar sarauta a jihar da ta ki ci ta ki cinyewa.

Kwankwaso ya ce Sanusi II Sarkin gwamnati ne Aminu Ado Bayero kuma na al'umma inda ya fayyace yadda za su gudanar da sallar idi.

Kara karanta wannan

Aiki zai dawo sabo: Gwamnoni 12 za su maka Tinubu a kotu kan Fubara

Musa Kwankwaso ya fadi sahihul Sarkin Kano
Musa Ilyasu Kwankwaso ya ce sun shirya fita sallar idi a Kano. Hoto: Sanusi Dynasty, Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Kwankwaso ya fadi Sarkin al'umma a Kano

Jigon APC ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na TikTok a jiya Alhamis 20 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musa Kwankwaso ya fadi lokacin da Aminu Ado Bayero zai fita filin idi domin salla karama yayin da Gwamna Abba Kabir ya ce sarakuna su shirya dawakai.

Ya ce Aminu Ado Bayero ne Sarkin al'umma wanda suka aminta da shi yayin da Sanusi II ya zama Sarkin gwamnati.

Abin da Musa Kwankwaso ya ce kan sallar idi

Musa Kwankwaso ya ce:

"A maganar sarauta an ce 'status quo', Aminu Ado shi ne Sarki, na ji Abba Kabir Yusuf ya ce a je a gyara dawakai.
"Ai daman ba wata matsala ba ce, su na da Sarkinsu Sanusi Lamido Sanusi, mu na Sarkinmu wanda al'umma suke so, Aminu Ado Bayero.

Kara karanta wannan

"Ina goyon bayan Tinubu": Kan gwamnoni ya fara rabuwa saboda dokar ta ɓaci a Ribas

"Amma lokaci zai yi, kamar yadda ka fada an ba da jadawali, ni ina ruwa na da wani jadawali.
"Ni Musa Ilyasu Kwankwaso a jadawali na Aminu Ado Bayero zai fita daga gidansa zuwa filin idi karfe 7.00 na da safe."
Kwankwaso ya bayyana yadda Aminu Ado zai gudanar da sallar idi
Musa Ilyasu Kwankwaso ya bayyana lokacin da Aminu Ado Bayero zai fita masallacin idi a ranar salla. Hoto: Musa Ilyasu Kwankwaso.
Asali: Facebook

Sallar Idi: Kwankwaso ya shawarci al'umma

Musa Kwankwaso ya ce ba fada suke nema ba, ya bukaci al'umma su fito sallar idi yana mai cewa babu ruwansu da wani Sanusi Lamido Sanusi.

Ya kara da ce babu ruwansu da maganar za a je can kafin a je can su kawai filin idi za su wuce kai tsaye.

An gargadi Abba Kabir kan rigimar sarauta

Mun ba ku labarin cewa yayin da ake dakon hukuncin kotun koli, Alhaji Aminu Babba Dan’agundi ya bukaci gwamnati da hukumomi su girmama umarnin kotun daukaka kara dangane da rikicin sarautar Kano.

Dan’agundi ya jaddada cewa doka ta bukaci a dawo da al’amura yadda suke kafin shari’ar ta fara a kotu kan rigimar da aka dade ana yi a Kano.

Jigon na APC a Kano ya bukaci wadanda aka nada bisa dokar 2024 su ajiye mukamansu domin girmama umarnin kotun daukaka kara har zuwa lokacin hukuncin Kotun Koli.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng