Mashahurin Ɗan Kasuwa kuma Malami a Kano, Nasiru Ahali Ya Rasu a Shekara 108

Mashahurin Ɗan Kasuwa kuma Malami a Kano, Nasiru Ahali Ya Rasu a Shekara 108

  • Shahararren malami kuma attajirin Kano, shugaban kamfanin Mainsara & Sons, Alhaji Nasiru Ahali, ya rasu yana da shekaru 108 a duniya
  • Ɗansa, Aminu Ahali, ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa, yana mai cewa ya rasu a wani asibiti da ke Kano da daren ranar Alhamis, 20 ga Maris
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana rasuwar Alhaji Nasiru Ahali a matsayin babban rashi ga Kano, Najeriya da al'ummar Musulmi duka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Shahararren attajirin nan na jihar Kano kuma shugaban kamfanin Mainsara & Sons, Nasiru Ahali, ya rasu yana da shekaru 108 a duniya.

Ɗansa, Aminu Ahali, ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa, yana mai cewa Alhaji Nasiru ya rasu a wani asibiti da ke Kano a daren ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Awanni da nada sababbin hadimai, Abba ya ba su umarnin bayyana yawan kadarorinsu

Kano: Iyalan Alhaji Nasiru Ahali, sun sanar da rasuwar mahaifinsu a daren ranar Alhamis.
Allah ya yiwa fitaccen dan kasuwar Kano, Alhaji Nasiru Ahali rasuwa yana da shekaru 108. Hoto: Real Kabeer Gashua
Asali: Facebook

Alhaji Nasiru Ahali ya rasu a jihar Kano

Marigayin yana daga cikin fitattun ‘yan kasuwa na farko a Kano da suka kafa kamfanoni da amfani da tsarin gudanarwa na zamani, inji rahoton Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce ya shahara a fannonin buga littattafai, ɗab’i, buga bulo, aikin ma'adinai, shigo da kaya, kwangiloli, gine-gine da sarrafa ƙarafa.

A lokacin da aka yi rikicin Maitatsine a Kano, an ce ‘yan tada zaune tsaye sun afka gidansa a ranar 18 ga Disamba, 1980, suka garkame iyalansa.

Daga bisani, ‘yan ta’addan sun kashe ‘ya’yansa biyu a wannan harin, lamarin da ya zama wani mummunan tarihi ga iyalansa.

Aminu Ahali, ya shaida cewa za a yi sallar jana’izar mahaifinsa a Masallacin Jumu’a na Nasiru Ahali da ke Kurna Asabe, bayan kammala Sallar Juma’a.

Gwamna Abba ya kadu da rasuwar Nasiru Ahali

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhinin sa kan rasuwar shahararren malamin addinin Islama kuma attajiri, Alhaji Nasiru Ahali.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe jami'an sojoji a wani kazamin farmaki da suka kai Benuwai

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafinsa na Facebook, Abba Yusuf ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi.

Ya ce mutuwar Alhaji Nasiru Ahali ba kawai rashi ne ga iyalansa ba, har ma ga jihar Kano, ƙasa baki ɗaya da kuma al'ummar Musulmi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin shuwagabannin masana'antu da suka assasa kasuwanci na zamani a Kano.

Gwamnan Kano ya yi wa marigayin addu'a

Gwamnan Kano, Abba Yusuf ya mika sakon ta'aziyyar rasuwar Alhaji Nasiru Ahali
Gwamnan Kano, Abba Yusuf tare da marigayi Alhaji Nasiru Ahali a wata ziyara da ya kai masa. Hoto: Real Kabeer Gashua
Asali: Facebook

Ya jaddada cewa marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin Kano da haɓaka manya da ƙananan masana'antu a jihar.

"A madadin gwamnatin Kano da al'ummar jihar, Gwamna Abba Kabir Yuuf na mika ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin da duk wanda mutuwar ta shafa.
"Ya yi addu’a ga Allah madaukaki da ya gafarta masa, ya jikansa da Rahama, ya kuma sa ya shiga Aljannatul Firdausi."

Kara karanta wannan

"Ka da a ɗora mun laifi": Gwamna Fubara ya cire tsoro, ya ƙaryata kalaman Tinubu

- A cewar sanarwar Sanusi Dawakin Tofa.

Fitaccen dan siyasa a Kano ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an yi jimami a Kano bayan rasuwar shahararren ɗan siyasa, Ahmadu Haruna Zago, wanda aka fi sani da Ɗanzago, bayan doguwar jinya.

Kafin rasuwarsa, Ɗanzago ya kasance shugaban hukumar kwashe shara ta Kano (REMASAB), inda ya jagoranci ayyukan tsaftar muhalli a jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel