Yakin Gaza: Najeriya Ta Fadi Yadda Ta ke Taimakon Falasdinawa

Yakin Gaza: Najeriya Ta Fadi Yadda Ta ke Taimakon Falasdinawa

  • Ministan harkokin kasar waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Najeriya ta taka muhimmiyar rawa a diflomasiyyar ceto jarirai daga Gaza
  • Najeriya ta yi nasarar kwashe jariran zuwa asibitoci a Jordan, Masar, da hadaddiyar daular larabawa domin ceto su daga luguden Isra'ila
  • Tuggar ya ce tun da fari, kungiyar bayar da agajin gaggawa a matakin farko ta Red Cross ta nemi Najeriya ta karbi wasu daga cikin jariran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Ministan harkokin kasar waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Najeriya ta taka muhimmiyar rawa a kokarin diflomasiyya na kwashe jarirai da kananan yara daga Gaza.

Ya bayyana cewa an yi nasarar kai jariran zuwa asibitoci a Jordan, Masar, da Hadaddiyar daular larabawa (UAE) yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta kan bayin Allah da ke Falasdinu.

Kara karanta wannan

'Me shirunsa ke nufi?' An taso Kwankwaso a gaba game da dokar ta ɓaci a Rivers

Tinubu
Najeriya ta taimaka wajen ceto jariran Gaza Hoto: One Path Netwrok/Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito Tuggar ya bayyana cewa wannan matakin ya biyo bayan bukatar da hukumar agajin gaggawa ta Redcross ta yi wa Najeriya na karbar wasu daga cikin yara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Najeriya ta ceto jarirai a Gaza

Tashar Trust TV ta ruwaito Tuggar ya bayyana yadda kungiyar Redcross ta nemi goyon bayan Najeriya wajen kwashe yaran da ke cikin mawuyacin hali na rashin lafiya.

Ya jaddada cewa Najeriya ta yi la'akari da yanayin lafiyar yaran da kuma wahalhalun da ke tattare da dauko su daga Gabas ta Tsakiya zuwa Najeriya.

Tinubu
Najeriya ta bi hanyar diflomasiyya wajen kwaso yaran Gaza zuwa wasu kasashe Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya ce:

“Kungiyar Red Cross ta tuntube mu, ta na tambaya ko Najeriya za ta iya karɓar wasu daga cikin jariran daga Gaza, domin suna neman kasashen da suka nuna damuwa kan halin da ake ciki a yankin.
“Amsarmu ita ce ba za mu iya ɗaukar wannan hadari ba, domin wasu daga cikin yaran suna da larurar zuciya tun daga haihuwa. Idan wani abu ya faru a hanya, mutane za su tambaya dalilin da ya sa muka ɗauki irin wannan haɗari, musamman ganin cewa muna da kalubale a bangaren kiwon lafiya."

Kara karanta wannan

Rivers: Atiku ya sauya salo, ya roƙi ƴan Najeriya bayan Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci

Yadda Najeriya ta ke taimakon Gaza

Ministan ya ce gwamnatin Najeriya ta yi amfani da hanyoyin diflomasiyya don tattaunawa da gwamnatocin Jordan, UAE, da Masar, inda ta nemi su karbi yaran domin kula da lafiyarsu.

Tuggar ya kara da bayyana cewa:

“Mun yi amfani da hanyoyinmu na diflomasiyya don tattaunawa da ministocin harkokin wajen waɗannan kasashe, inda muka jaddada musu muhimmancin karɓar yaran da kuma samar musu da kulawar lafiya. Kuma alhamdulillah, an samu nasara.”

Gwamnatin Najeriya ta tsoma baki kan rikicin Gaza

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Najeriya ta bukaci Isra'ila da Gaza su tabbatar an aiwatar da matakai na biyu da na uku na yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla a tsakanin bangarorin.

Haka kuma kasar nan ta bayyana goyon bayanta ga mafita ta kasashe biyu a matsayin hanyar samar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin Falasdinawa da Isra'ila don rage kisan jama'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng