Bidiyo: Yadda Mutane 10 Suka Mutu, Motoci 18 Suka Kone Kurmus a kan Gadar Abuja
- Wata motar dakon siminti ta kama da wuta a kan titin Abuja-Keffi, lamarin da ya haddasa mutuwar mutum 10 da konewar motoci 18
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban, yayin da gobarar ta haddasa cunkoso
- Hukumar bayar da jini ta ƙasa (NBSA) ta yi kira ga al'umma da su bayar da gudunmawa domin taimaka wa waɗanda suka jikkata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wani mummunan hatsari ya faru a gadar Karu da ke kan titin Abuja-Keffi, inda motar dakon siminti ta kama da wuta bayan ta yi taho-mu-gama.
Hukumar bada agajin gaggawa ta Abuja (FEMA) ta tabbatar da mutuwar mutum 10 da konewar motoci 18 a gobarar da ta tashi bayan hadarin.

Kara karanta wannan
Wuri ya yi wuri: An daka wawar kayan abinci a motar Majalisar Dinkin Duniya a Borno

Asali: Twitter
Hatsari a hanyar Abuja-Keffi ya haddasa cunkoso
Rahotan The Nation ya bayyana cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin kasa, asibitin Karu da asibitin fadar shugaban kasa domin samun kulawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shaidun gani da ido sun ce gobarar ta haddasa cunkoson ababen hawa, inda matafiya suka tilasta wa kansu tafiya a ƙafa domin isa gidajensu.
Stephen Ogidi, wani mazaunin Karu, ya bayyana cewa akwai buƙatar samar da wata hanyar da matafiya za su rika bi madadin titin Abuja-Keffi domin rage cunkoso.
Ya ce:
“Hatsarin ya faru ne kamar a fim. Mun ga mutane suna ta gudu ta ko ta ina domin ceton ransu. An samu cunkoso sosai, har ba a iya wucewa, kuma babu wata hanya ta zagaye wa."
Matafiya sun nemawa kansu mafita bayan hatsari
Ogidi ya soki yadda gwamnatin jihar Nasarawa ta gaza samar da wata hanya ta rage cunkoson ababen hawa daga yankin zuwa Abuja.
Matafiya daga Nyanya da Maraba sun sha wahala a wannan rana, inda aka hango mata da yara suna tafiya da ƙafa da misalin karfe 2:00 na dare.
Motocin haya sun ƙi daukar mutane saboda cunkoson titin, lamarin da ya haddasa rashin ababen hawa da wahalar sufuri ga matafiya.
Wasu direbobi sun gaza jure wannan cunkuso, suka fara ratsewa ta cikin barauniyar hanya domin su tsira daga turmutsutsin da hatsarin ya haddasa.
Abuja-Keffi: Mutane 10 sun mutu a hatsarin mota

Asali: Twitter
A farkon rahoto, rundunar ‘yan sandan Abuja ta ce mutum shida ne suka mutu, amma daga bisani hukumar FEMA ta tabbatar da mutuwar mutane 10.
Hukumar bayar da jini ta ƙasa (NBSA) ta yi kira ga masu ƙoshin lafiya da su bayar da gudunmawar jini domin ceto rayukan wadanda suka jikkata.
Daraktan hukumar, Farfesa Saleh Yuguda, ya ce yawancin waɗanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali kuma suna buƙatar jini cikin gaggawa.
"Asibitoci na ƙoƙarin ceto rayukan wadanda suka jikkata, amma muna buƙatar isasshen jini. Muna kira ga masu lafiya su ziyarci cibiyoyin bada jini."
- Farfesa Saleh.
Kalli yadda hatsarin ya afkuwa da abin da ya biyo baya nan kasa:
Gwamnati na karbar haraji a hanyar Abuja-Keffi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta fara karɓar harajin hanyar Abuja-Akwanga-Lafia-Makurdi daga direbobi da ke amfani da titin.
Ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa kananan motoci za su biya N500, yayin da manyan motoci za su biya N1,600 a kowace tafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng