Rivers: An Shiga Fargabar Halin da Fubara Ya Shiga Kwanaki 2 bayan Dakatar da Shi

Rivers: An Shiga Fargabar Halin da Fubara Ya Shiga Kwanaki 2 bayan Dakatar da Shi

  • Ɗaya daga cikin ƴan gwagwarmaya a yankin Neja Delta, Cif Anabs Sara-Igbe, ya nuna damuwa kan halin da Gwamna Simi Fubara yake ciki
  • Ɗan gwagwarmayar ya nuna cewa har yanzu ba a ji ɗuriyar gwamnan ba kwanaki biyu bayan an dakatar da shi daga muƙaminsa
  • Ya buƙaci ƴan Najeriya da su fito su yi adawa da dokar ta ɓacin da aka ƙaƙaba a jihar Rivers, domin barazana ce ga mulkin dimokuraɗiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Ɗan gwagwarmaya kuma ɗaya daga cikin dattawan yankin Neja Delta, Cif Anabs Sara-Igbe, ya nuna damuwa kan inda Gwamna Siminalayi Fubara ya shiga.

Cif Anabs Sara-Igbe ya bayyana cewa mutanen jihar Rivers na cikin damuwa game da inda Gwamna Siminalayi Fubara yake, bayan dakatar da shi daga muƙaminsa.

An nemi Gwamna Fubara an rasa
An koka kan rashin sanin inda Gwamna Fubara yake Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da tashar Arise Tv a ranar Alhamis, 20 ga watan Maris 2025.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya naɗa sababbin mukamai, tsohon mai adawa da gwamnati ya rabauta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Talata, 18 ga watan Maris, 2025, shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Fubara, mataimakiyarsa, Ngozi Odu, ƴan majalisar dokokin jihar Rivers saboda rikicin siyasa da ya ta'azzara a jihar.

Bayan wannan mataki da shugaban ƙasan ya ɗauka, an ga gwamnan da iyalansa da jami’an tsaronsa su na barin gidan gwamnatin jihar.

An nemi Gwamna Fubara an rasa

Sai dai, a yayin hirar, Sara-Igbe ya ce babu wanda ya ga ko ya ji daga Gwamna Fubara har yanzu.

Ya ce rayuwar Fubara na cikin haɗari, kuma shugabannin Rivers sun yi ƙoƙarin tuntuɓarsa amma ba su samu damar yin hakan ba.

“Muna cikin damuwa saboda ba mu ga Fubara ba, kuma babu wanda ya samu damar yin magana da shi. Ba mu san abin da suka yi masa ba, ba mu san inda yake ba. Don haka, rayuwarsa na cikin haɗari."
"Mun yi ƙoƙarin tuntuɓarsa, amma ba mu samu nasara ba. Duk ƴan Najeriya su sani cewa rayuwar Fubara na cikin haɗari. Har sai mun ga Fubara ya yi magana kai tsaye ko a talabijin, sannan za mu amince da cewa yana cikin ƙoshin lafiya".

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamnatin Tinubu ta fadi gatan da za ta yi wa 'shugaban rikon kwarya'

"Ba mu ji daga gare shi ba. Da gaske ku tambaya ku ji ko akwai wanda ya ji daga gare shi. An kulle shi a gidan gwamnati, mun dai ga hotunansa a shafukan sada zumunta, amma bayan an ce an sake shi daga gidan gwamnati, zuwa ina?"
"Ba mu sani ba. Mutanen Rivers na cikin fargaba. Wannan ba yaƙi ne da Fubara kaɗai ba, yaki ne da jihar Rivers."

- Anabs Sara-Igbe

An yi kira ga ƴan Najeriya kan Rivers

Sara-Igbe ya buƙaci ƴan Najeriya da su fito domin nuna adawa da abin da ya kira “dakatarwa ba bisa ƙa’ida ba” da aka yi wa Fubara.

“Ina kira ga ƴan Najeriya da su fito su nuna adawa da wannan haramtacciyar dakatarwar. Idan ƴan Najeriya suka yi shiru suka bar wannan abu ya faru, to zai faru a sauran wurare."

- Anabs Sara-Igbe

Majalisa ta amince da bukatar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilan Najeriya ta yi muhawara kan dokar ta ɓacin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sanya a jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Rivers: Abin da manyan lauyoyi ke cewa kan matakin Tinubu na sa dokar ta baci

Majalisar wakilan ta amince da dokar ta ɓacin da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya a jihar da ke yankin Kudu maso Kudu mai arziƙin mai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng