Wuri Ya Yi Wuri: An Daka Wawar Kayan Abinci a Motar Majalisar Dinkin Duniya a Borno

Wuri Ya Yi Wuri: An Daka Wawar Kayan Abinci a Motar Majalisar Dinkin Duniya a Borno

  • Wasu da ba a san ko su wanene ba sun kwace wata motar tallafin kayan abinci ta hukumar WFP a garin Gubio a jihar Borno
  • Motar na kan hanyar zuwa Damasak lokacin da direbanta ya tsaya a gefen hanya, babu kowa a ciki lokacin da aka yi aika-aikan
  • Miyagu sun sace buhunan shinkafa, gishiri, sukari, wake da kuma man gyada wanda ba a san yawan su ba zuwa yanzu tukuna
  • Jami’an tsaro sun kai ziyara wurin da abin ya faru, amma har yanzu ba a kama kowa ba sai dai bincike na ci gaba da gudana

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Wata mota mai dauke da kayan abinci na shirin tallafi na World Food Programme (WFP) ta fada hannun barayi a Gubio da ke jihar Borno.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

Rahotanni sun tabbatar da cewa an daka wawa kan kayan abinci da suka hada, shinkafa, sukari, wake da sauransu.

Mutane sun sace kayan abinci a korar hukumar WFP a Borno
Wasu mutane sun daka wawa kan kayan abinci a motar hukumar WFP a Borno. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum, @ZagazOlamakama.
Asali: Facebook

An kawo tallafin abinci a Arewacin Najeriya

Majiyoyin sirri sun shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya faru misalin karfe 2:30 na rana a lokacin da direban motar, Aminu Mallam Umar, ya tsaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan Bankin Raya yankin Nahiyar Afirka (AfDB) ya bayar da tallafin $1m domin rage yunwa a wasu jihohin Arewacin Najeriya.

Rahotanni sun ce Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) tana aiki da gwamnatin Najeriya don taimaka wa al'ummomin da ambaliya ta shafa.

Ana hasashen cewa mutane aƙalla miliyan 33 ka iya fuskantar matsalar rashin abinci nan da watan Agustan shekarar 2025 da muke ciki.

Mutane sun daka wawa, sun kwashe kayan abinci a Borno
Ana ci gaba da bincike bayan kwashe kayan abinci a motar hukumar WFP a Borno. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Asali: Original

Hakan bai rasa nasaba da wahalar da ake ciki a halin yanzu na tsadar kayan abinci musamman a wannan wata na Ramadan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya za ta raba tallafin kudin noma ga mutane 250,000

Rahotanni sun ce Arewacin Najeriya na daga cikin yankin da zai fuskanci yunwa a 2025 da talauci wanda ke kara ta'azzara da kuma sake jefa yankin a matsalolin tsaro da ake ciki.

WFP: Yadda aka kwashe kayan abinci a Borno

Lokacin da babu kowa a cikin motar, wasu da ba a san ko su waye ba sun sace buhunan shinkafa, gishiri, sukari, wake da man gyada.

Jami’an tsaro sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, amma ba a kama kowa ba yayin da ake dakon bayanai kan yawan asarar da hakan ya jawo.

Sojoji sun fitar da motar zuwa Gubio yayin da bincike ke ci gaba da gudana domin zakulo wadanda suka aikata laifin.

Gwamna Zulum ya yi wa ƴan kasuwa rangwame

Kun ji cewa Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya yi wa ƴan kasuwan da ambaliyar ruwa da kuma gobara ta shafa rangwame.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya ɗauki matakin ƙarshe, ya fice daga gidan gwamnatin jihar Ribas

Gwamna Zulum ya amince da janyewa ƴan kasuwan biyan kuɗin haraji har na tsawon shekaru biyu domin sauƙaƙa musu kan asarar da suka yi yayin iftila'in da ya faru.

Rahotanni sun ce yan kasuwan da za su ci gajiyar wannan rangwamen, sun haɗa da wadanda gobara ta shafa a kasuwar Monday Market da ke birnin Maiduguri.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng