Gwamnatin Najeriya za Ta Raba Tallafin Kudin Noma ga Mutane 250,000

Gwamnatin Najeriya za Ta Raba Tallafin Kudin Noma ga Mutane 250,000

  • Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shiri domin tallafa wa manoma 250,000 a kokarin tabbatar da wadatar abinci da ci gaban tattalin arziki
  • Ministan tattalin arziki, Wale Edun, ya ce shirin zai kunshi bayar da kayan aiki, tallafin kudi, da inganta hanyoyin ajiyar kayan amfanin gona
  • Rahotanni sun nuna cewa shirin ya samu goyon bayan Japan da Brazil, za a mayar da hankali kan noma shinkafa, masara, rogo da dawa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta tallafa wa manoma 250,000 domin bunkasa harkar gona a Najeriya.

Ministan Kudi kuma Ministan Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Wale Edun, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da shirin NAGS a ranar Laraba a Abuja.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

Bola Tinubu
Gwamnatin Najeriya za ta raba tallafin noma. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar the Cable ta wallafa cewa daraktan yada labarai na ma’aikatar, Mohammed Manga ne ya fitar da sanarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed Manga ya bayyana cewa shirin na daga cikin matakan gwamnatin Bola Tinubu na habaka tattalin arziki da tabbatar da wadatar abinci.

Raba tallafin kayan aiki da kudi ga manoma

Mista Edun ya ce shirin zai taimaka wajen habaka noman zamani ta hanyar bayar da kayan aikin gona, tallafin kudi, da kuma inganta hanyoyin ajiyar kayayyakin amfanin gona.

Ya kara da cewa shirin zai samu tallafin kudi daga Japan International Cooperation Agency (JICA) da kuma shirin hadin gwiwa da Brazil.

Wale Edun ya bayyana cewa za a bai wa manoma 200,000 tallafi a lokacin damina, sannan 50,000 a lokacin rani.

Ya kara da cewa za a fi maida hankali kan amfanin gona irin su shinkafa, masara, rogo da dawa, domin habaka samar da wadataccen abinci da rage hauhawar farashi a kasuwa.

Kara karanta wannan

Dakatar da Fubara: Da gaske 'yan Neja Delta sun kai hari matatar Fatakwal?

Muhimmancin hadin gwiwa a fannin noma

Babban sakataren Hukumar Raya Kasar Noma (NALDA), Cornelius Adebayo, ya ce hadin gwiwar gwamnati da masu ruwa da tsaki zai taimaka wajen rage matsalolin da manoma ke fuskanta.

Ya ce shirin zai magance matsaloli kamar rage asarar amfanin gona bayan girbi, daidaita farashin kayayyakin noma, da kuma inganta hanyoyin rarraba kayayyakin abinci zuwa kasuwanni.

Adebayo ya ce wannan shiri zai taimaka wajen bunkasa tsarin ajiyar kayan abinci a kasa, wanda zai kara karfin ajiyar abinci na kasa domin kauce wa karancin abinci a nan gaba.

Shirin rage matsalolin rarraba kayan noma

A yayin taron, mahalarta sun tattauna kan matsalolin da suka shafi rarraba kayayyakin abinci daga gonaki zuwa kasuwanni.

Ma’aikatar kudi ta tabbatar da cewa gwamnati na daukar matakai don tabbatar da wadatar abinci, habaka tattalin arziki, da inganta rayuwar manoma da al’ummar Najeriya gaba daya.

Kara karanta wannan

Wuri ya yi wuri: An daka wawar kayan abinci a motar Majalisar Dinkin Duniya a Borno

Ministan Kudi
Ministan kudin Najeriya, Wale Edun. Hoto: Federal Ministry of Finance
Asali: Getty Images

'Yan Najeriya sun zuba ido wajen jin hanyoyin da za su wajen ganin sun shiga cikin shirin domin damawa da su.

Legit ta tattauna da manomi

Wani manomi a jihar Gombe, Haruna Abdullahi ya bayyanawa Legit cewa tallafin zai taimaka matukar zai iso gare su.

"Manoma masu karamin karfi iri na za su amfana da tallafin, ina kira ga gwamnati ta tabbatar da kudi da kayan aikin sun isa hannun manoman gaskiya"

- Haruna Abdullahi

Haruna ya ce idan kudi da kayan ba su shiga hannun da ya dace ba, ba za a samu nasarar samar da abinci da shirin ke fatan samar wa ba.

Sanata Barau Jibrin zai raba tallafin noma

A wani rahoton, kun ji cewa an bude shafin yanar gizo domin cike shirin tallafin noma na Sanatan Kano ta Arewa, Barau I. Jibrin.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa shirin tallafin zai shafi matasa da ke yankin Arewa ta Yamma ne kai tsaye.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng