Rikicin Rivers: Tinubu Ya Dakatar da Gwamna Fubara, Ya Nada Sabon Shugaba

Rikicin Rivers: Tinubu Ya Dakatar da Gwamna Fubara, Ya Nada Sabon Shugaba

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki mataki kan rikicin siyasar da ya addabi jihar Rivers mai arziƙin mai
  • Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci a jihar bayan abubuwa sun dagule tsakanin Gwamna Simi Fubara da majalisar dokoki
  • Mai girma Shugaban ƙasan ya kuma dakatar da gwamnan tare da mataimakiyarsa har na tsawon watanni shida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci a jihar Rivers da ke yankin Kudu maso Kudu na Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa, Mrs Ngozi Odu, na tsawon watanni shida.

Tinubu ya sa dokar ta baci a Rivers
Tinubu ya dakatar.da Gwamna Siminalayi Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe a cikin jawabin da shugaban ƙasan ya yi ga ƴan Najeriya a yammacin ranar Talata, 18 ga watan Maris 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin shugaba Bola Tinubu kan harkokin kafofin sadarwa na zamani, Dada Olusegun ya sanya jawabin shugaban ƙasan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Rikicin Ribas: An ƙara samun bayanai kan dalilin shugaba Tinubu na dakatar da gwamna

Meyasa Tinubu ya sa dokar ta ɓaci?

Tinubu ya ce an ɗauki wannan matakin ne domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar, wacce ke fama da rikicin siyasa sakamakon rashin jituwa tsakanin gwamnan jihar da ƴan majalisar dokoki.

"Da wannan sanarwa, an dakatar da gwamnan jihar Rivers, Mr Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, Mrs Ngozi Odu, da dukkan zaɓaɓɓun ƴan majalisar dokokin jihar Rivers na tsawon watanni shida."

- Gwamna Siminalayi Fubara

Shugaban ƙasan ya naɗa Vice Admiral Ibok-Ette Ibas (mai ritaya) a matsayin wanda zai ci gaba da kula da harkokin mulki a jihar.

"A halin yanzu, na naɗa Vice Admiral Ibok-Ette Ibas (mai ritaya) a matsayin mai kula da harkokin jihar, domin jagorantar al’amuran mulki a jihar don amfanin jama’ar Rivers."
"Domin a kawar da duk wani shakku, wannan sanarwa ba ta shafi ɓangaren shari’a na jihar Rivers ba, wanda zai ci gaba da aiwatar da aikinsa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada."

Kara karanta wannan

Jonathan ya tsoma baki kan dakatar da Fubara, ya fadi illar hakan ga Najeriya

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya yi amfani da tanadin kundin tsarin mulki

Shugaban ƙasa ya ambaci sashe na 305 na kundin tsarin mulki na 1999, yana mai cewa ɗaukar wannan matakin na gaggawa ya zama dole domin dawo da zaman lafiya.

Ya ƙara da cewa an wallafa wannan sanarwar a cikin jaridar gwamnati (Federal Gazette) tare da aikawa ga majalisar dokoki ta ƙasa.

"Fatan da nake yi shi ne wannan mataki da aka ɗauka zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya da doka a jihar Rivers."
"Hakan na da muhimmanci domin tunatar da dukkanin ɓangarorin muhimmancin bin tanadin kundin tsarin mulki a kan dukkanin masu ruwa da tsaki na siyasar Rivers da Najeriya ba ki ɗaya."

- Shugaba Bola Tinubu

Mun shiga halin rashin tabbas

Paul Ugorji wani mazaunin birnin Port Harcourt ya bayyana cewa sun shiga halin rashin tabbas sakamakon dokar ta ɓacin da aka ayyana

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun faɗi damuwarsu kan dokar ta ɓaci a Ribas, sun ambaci Kano

"Ba mu san abin da zai faru ba, mun ga motocin sojoji suna ta wucewa da jiniyoyi."
"Ina ganin dokar ta ɓacin nan da aka sanya akwai siyasa a ciki. Kowane ɓangare yana da na shi laifin."
"Muna fatan abubuwa su daidaita zuwa nan da wata shida lokacin da dokar ta ɓacin za ta daina aiki."

- Paul Ugorji

An fara shirin tsige Gwamna Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan majalisar dokokin jihar Rivers sun fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara daga kan muƙaminsa.

Ƴan majalisar dokokin na jihar Rivers sun aika da wasiƙa ga gwamnan wacce ke ƙunshe da zarge-zargen da suke yi masa.

Idan zarge-zargen dai suka tabbata, Gwamna Fubara na iya rasa kujerarsa daga nan zuwa tsakiyar watan Yulin 2025.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng