Zargin Wawushe Kudi: Ciyamomin Kaduna Sun Karyata El Rufai, Sun Kare Uba Sani

Zargin Wawushe Kudi: Ciyamomin Kaduna Sun Karyata El Rufai, Sun Kare Uba Sani

  • Shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kaduna, sun fito sun yi martani kan zargin da Nasir El-Rufai ya yi a kan gwamnati
  • Ciyamomin a ƙarƙashin ƙungiyar ALGON sun musanta cewa gwamnatin Uba Sani na wawushe kuɗin ƙananan hukumomin Kaduna
  • Shugabannin kananan hukumomin sun bayyana cewa zargin da tsohon gwamnan ya yi, babu ƙamshin gaskiya ko kaɗan a cikinsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta Najeriya (ALGON), reshen jihar Kaduna, ta yi martani kan zargin da Nasir El-Rufai ya yi wa gwamnatin Uba Sani.

Ƙungiyar ALGON ta yi watsi da zargin da tsohon gwamnan ya yi na cewa ana karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar.

ALGON ta kare Uba Sani
ALGON ta musanta zargin El-Rufai kan Uba Sani Hoto: @ubasanius, @elrufai
Asali: Twitter

Kakakin ALGON, Alhaji Muhammad Lawal Shehu ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

El Rufai ya tono yadda ake ruf da ciki da kudin Kaduna a mulkin Uba Sani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ALGON ta ƙaryata zargin El-Rufai kan Uba Sani

ALGON ta bayyana zarge-zargen a matsayin waɗanda ba su da tushe, ba su da ma’ana, kuma an yi su ne da mugun nufi.

Kakakin na ALGON ya bayyana cewa zarge-zargen an yi su ne domin yaudarar jama’a, haifar da rarrabuwar kawuna, da kuma ɓata sunan gwamnatin Uba Sani, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

"Gwamnatin Gwamna Uba Sani ta na bin doka da ƙa’ida. Babban ginshiƙin mulkinsa shi ne gaskiya da riƙon amana.
Ya na mutunta ƴancin ƙananan hukumomi, kuma ba ta taɓa yin babakere a cikin kuɗaɗen su ba."

- Alhaji Muhammad Lawal Shehu

Alhaji Muhammad Lawal Shehu ya ƙara da cewa, akasin zargin da ake yi, gwamnatin Uba Sani ta na aiwatar da shirye-shirye da ayyukan da ke ƙarfafa ƙananan hukumomi.

"Mu da mu ke magana a yau, wasu daga cikinmu mun riƙe muƙamin shugabannin ƙananan hukumomi lokacin da Malam Nasir El-Rufai ke gwamna."

Kara karanta wannan

El Rufai ya sake bankado babban lamari, ya zargi Gwamna Uba da 'Satar' kuɗin Kaduna

"Muna iya tabbatar da cewa kuɗin da mu ke karɓa a matsayin kasonmu na wata-wata tun bayan da Sanata Uba Sani ya hau mulki sun fi ninkin abin da muke samu a zamanin El-Rufai."
"Ba wai kawai an ƙara kuɗin wata-wata ba, har ma mu na gudanar da ayyukanmu ba tare da tsangwama da danniya ba."
"Ba haka lamarin yake ba a lokacin mulkin Malam Nasir El-Rufai, inda aka sha yin amfani da iko fiye da ƙima don matsawa shugabannin ƙananan hukumomi lamba."

ALGON ta buƙaci a yi watsi da maganar El-Rufai

A ƙarshe, ALGON ta bayyana cewa ta maida hankali wajen tunkarar matsalolin da ke fuskantar al’ummar Kaduna tare da cikakken goyon bayan Gwamna Uba Sani.

"Muna ba da cikakken goyon baya ga Gwamna Uba Sani. Babu wani abu da gwamnati ta yi wanda ya sa muka koka."
"Don haka, muna kira ga jama’a da su yi watsi da maganganun da aka danganta da Malam Nasir El-Rufai, domin ba su da tushe ko wata hujja da ke tabbatar da su."

Kara karanta wannan

El Rufai ya fara karɓe magoya bayan Kwankwaso, jiga jigan NNPP sun koma SDP

- Alhaji Muhammad Lawal Shehu

El-Rufai ya zargi Uba Sani da karɓo kwangila

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya zargi Uba Sani da karɓo kwangila domin karya shi a siyasance.

El-Rufai ya yi zargin cewa Gwamna Uba Sani ya karɓo kwangila ne daga shugaba Bola Tinubu domin ya ɓata masa suna kafin zabe mai zuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel