Tinubu Ya Samu Yadda Yake So, Majalisa Ta Dauki Matakin Karshe kan Kudirin Haraji
- Majalisar wakilan Najeriya ta amince da ƙudirorin gyaran haraji da gwamnatin tarayya ta gabatar mata a kwanakin baya
- Amincewa da ƙudirorin na zuwa ne bayan sun tsallake karatu na uku a zauren majalisar yayin zamanta na ranar Talata, 18 ga watan Maris 2025
- Majalisar ta amince da ƙudirorin ne bayan kwamitinta kan kuɗi ya gabatar da rahotonsa kan jin ra'ayoyin jama'a da ya yi dangane da ƙudirorin
- Kafin amincewa da ƙudirorin, an yi musu kwaskwarima inda aka cire wasu sassa yayin da wasu sassan kuma aka yi musu gyare-gyare
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Majalisar wakilan Najeriya ta amince da ƙudirorin gyaran haraji guda huɗu da aka gabatar mata.
Majalisar ta amince da ƙudirorin ne bayan sun tsallake karatu na uku a ranar Talata, 18 ga watan Maris 2025.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an amince da su ne bayan nazarin da majalisar ta yi musu a baya a ranar Alhamis da ta gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kuɗirin haraji ya tsallake karatu na 3 a majalisa
Idan za a iya tunawa cewa majalisar ta duba ƙudirorin, sashe bayan sashe, a ranar Alhamis da ta gabata bayan da ta karɓi rahoton sauraron ra’ayoyin jama’a da kwamitin majalisa kan kuɗi ya shirya.
Gwamnatin tarayya ta aika da ƙudirorin ga majalisar dokoki ta ƙasa a watan Oktoban 2024.
Waɗannan ƙudirori sun haifar da cece-kuce, ƙin amincewa da su, da kuma shakku daga ƙungiyoyi, ƴan kasa daban-daban, da kuma yankuna daban-daban na ƙasar nan.
Hakan ya sa aka gudanar da shawarwari, yin tattaunawa a matakai daban-daban, wanda daga ƙarshe ya kai ga sauraron ra’ayoyin jama’a domin bai wa kowa damar bayyana matsayarsa.
Daga bisani, an yi wa abubuwan da ƙudirorin suka ƙunsa gyare-gyare ta hanyar tsarin dokoki, wanda ya haɗa da yin kwaskwarima.
Hakazalika an cire wasu sassa, da kuma ƙara sababbin sassa da ƙananan sassa kamar yadda kwamitin majalisar kan kuɗi ya gabatar.
Daga ƙarshe, majalisar ta karɓi rahoton, ta amince da gyare-gyaren, kuma sun tsallake karatu na uku.
Karanta wasu labaran kan ƙudirin haraji
- Kungiyoyin Arewa sun bijirewa ƙudirin haraji, sun faɗi illarsa ga talaka
- Kudirin haraji zama daram," da abubuwa 3 da Tinubu ya faɗa a kan manufofinsa
- An ba Tinubu gurguwar shawara," Ɗan majalisa ya tona kura kuran da aka gano a ƙudirin haraji
Ƴan majalisa sun ba Tinubu gudunmawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan majalisar wakilan Najeriya sun cika alƙawarin da suka ɗauka kan albashinsu a watannin baya.
Ƴan majalisar sun raba albashinsu gida biyu, suka ba da shi ga shugaba Bola Tinubu domin zama tallafi ga ƴan Najeriya.
A yayin wata liyafar buɗa baki da shugaba Bola Tinubu ya shiryawa ƴan majalisar, shugaban majalisar, Tajudeen Abbas ya gabatar da takardar kuɗi ta banki ta N750m ga shugaban ƙasan.
Ba da kuɗin ya zama cika alƙawarin da ƴan majalisar suka ɗauka na raba albashinsu domin taimakawa ayyukan ba da tallafu ga ƴan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng