Shigo da Mai: Kotu Ta Yi Hukunci a Takaddamar NNPCL da Matatar Dangote
- Kotun Tarayya ta kori korafin NNPCL da ke ƙalubalantar cancantar karar da matatar Aliko Dangote ta shigar kan lasisin shigo da kaya
- Alkalin kotun ya ce kamfanin NNPCL ya karya dokokin shari’a, inda ya kasa gabatar da bayanai da kuma shigar da ƙara marar inganci
- Mai shari’a ya bayyana cewa kotu na da damar warware batun ikon sauraron ƙara lokacin yanke hukunci, ba sai tun farko ba
- Kotu ta amince da Dangote ya gyara karar don saka sunan NNPCL daidai, tana mai cewa hakan babu cutarwa a ciki dangane da adalci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya ta yi zama kan takaddamar da ake yi tsakanin kamfanin mai na NNPCL da matatar Aliko Dangote.
Kotun ta kori karar da kamfanin NNPCL ya shigar na bukatar soke korafin da matatar Dangote ta gabatar.

Kara karanta wannan
"Ba ka yi mana adalci ba," NLC ta yi raddi ga Obasanjo kan mafi karancin albashin N70,000

Asali: Facebook
Matatar Dangote ta shigo da mai daga ketare
Mai shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yi fatali da korafin NNPCL ta farko kan matatar Dangote, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan Matatar Dangote ta sayi ganga 950,000 na danyen man Ceiba daga Equatorial Guinea, wanda zai iso matatar tsakanin 12 zuwa 13 ga watan Afrilun 2025.
Rahotanni sun nuna cewa NNPCL ya aika da jiragen ruwa dauke da danyen mai zuwa matatar Dangote domin ci gaba da sarrafawa a Najeriya.
Attajirin nahiyar Afrikan ya bayyana cewa matatar tana shirin kai cikakken ƙarfin tace mai a watan Maris din 2025.

Asali: Facebook
Dangote/NNPCL: Wane hukunci kotun ta yi?
A hukuncin da ya yanke, mai shari’a Ekwo ya ce NNPCL ta kasa shigar da ƙarin bayani, sai dai kawai ta shigar da ƙara marar ƙarfi.
Alkalin ya ƙara da cewa idan aka gabatar da batun ikon sauraron ƙara, kotu na iya warware shi a lokacin da ake yanke hukunci.
Ya soki NNPCL da karya dokar matsayi ta 16 ta Babbar Kotu, inda ya ce ƙarar da ta shigar ba ta cika ka’idar doka ba, Punch ta ruwaito.
Mai shari’a Ekwo ya bayyana cewa NNPCL ba zai gamu da rashin adalci ba idan Dangote ya canza sunan kamfanin cikin takardarsa.
Dangane da buƙatar gyara sunan NNPCL a cikin karar, mai shari’a ya ce gyaran da Dangote ya nema yana da yiwuwar amincewa da shi.
A ƙarshe, kotun ta amince da gyaran da matatar Dangote ta nema, aka tabbatar da sabunta karar daidai da doka.
Dangote ya zargi tsohon gwamna da kassara shi
A wani labarin, Alhaji Aliko Dangote ya zargi tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, da yi masa illa bayan rushe masa aikin ginin sabon masana’antar siminti har sau biyu.
Attajirin ya ce sun dawo ci gaba da aikin a jihar Ogun ne saboda manufofin Gwamna Dapo Abiodun da yanayin da ya dace da masu zuba jari a jiharsa.

Kara karanta wannan
Sanata Natasha ta shiga matsala, DSS, NIA sun fara bincikar ta kan zuwa taron IPU
Gwamna Abiodun ya bayyana cewa gwamnatin Amosun ta hana ci gaban masana’antar har sau uku, ciki har da ginin matatar mai a Legas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng