'Yadda Ribadu Ya Hada Kai da ICPC domin Kai Ni Kurkuku kafin Zaben 2027', El Rufai
- Nasir El-Rufai ya zargi Nuhu Ribadu da shirya makarkashiyar tura shi gidan yari kafin zaben 2027 ya karaso
- El-Rufai ya ce Ribadu na kokarin lalata masa suna saboda tsoron ka da ya hana su cin nasara a zabukan gaba
- Tsohon gwamnan ya ce an ba Gwamna Uba Sani kwangilar rubuta rahoto na bogi don kai shi kasa, bisa umarnin Ribadu
- Ya bayyana cewa 'yan majalisar jihar Kaduna ba su da isasshen ilimi har su iya rubuta irin wannan rahoto da kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya sake magana kan zargin makarkashiya da ake kulla masa.
El-Rufai ya zargi Nuhu Ribadu da neman kai shi kurkuku a shekarar 2025 saboda ka da ya jawo musu matsala a zaben 2027.

Asali: Twitter
'Makarkashiyar Uba Sani a kai na' - El-Rufai
El-Rufai ya bayyana haka ne a cikin wata hira da gidan rediyon Freedom da aka wallafa a shafin YouTube.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin faifan bidiyon, El-Rufai ya fadi yadda aka ba Uba Sani kwangilar kirkirar rahoto na musamman domin kai shi kasa.
Ya ce hakan ya biyo bayan umarnin Nuhu Ribadu ga shugaban hukumar ICPC wanda shi ne ya ba shi muƙamin tun farko.
Tsohon gwamnan ya kuma ce duk ƴan majalisar jihar Kaduna ba su da ilimin rubuta rahoton zargin da ake yi masa da kwamishinoninsa.
"Kamar yadda na fada, Uba Sani kwangila ya karba domin ya yi wannan rahoto, an kai rahoton ga ICPC da EFCC.
"Daga cikin ƴan majalisar babu mai ilimin da zai iya kama kwamishinoni na ko sun yi daidai ko ba daidai ba, saboda daga jahilai sai wadanda ke ilimin taro da sisi.
"Rahoton ma rubuta musu aka yi saboda dukansu babu mai ilimin da zai iya rubuta wannan rahoto."

Kara karanta wannan
"40% ake ba shi," El Rufai ya zargi Uba Sani da yin kashe mu raba da ƴan kwangila

Asali: Facebook
Zargin da El-Rufai ke yi wa Ribadu
El-Rufai ya zargi Nuhu Ribadu da tilasta shugaban ICPC ya nemi laifi ya lika wa mutanensa da kuma shi kaina.
El-Rufai ya kara da cewa:
"Shugaban ICPC na yanzu kanin Faruk Adamu Aliyu ne wanda shi kuma aminin Nuhu Ribadu ne.
"Ribadu ne ya samo wa wannan yaro aiki kuma ya ce masa dole ya samu laifi ya lika mani da kuma mutanena saboda burinsu shi ne a kai ni kurkuku a cikin wannan shekarar 2025.
"Duk wannan tsarin Nuhu Ribadu saboda ka ka da na kawo musu matsala a zabensu inda ya hada kai Uba Sani a Kaduna."
Ana binciken ayyukan El-Rufai a 2000
El-Rufai ya ce da aka gaza samun wani abu Kaduna har hukumar BPE da ya yi aiki tun 2003 aka je ana binciken kudin guzurin da aka ba shi.
Ya ce bayan an je Abuja babu komai shi ne aka koma BPE inda ya ce yanzu saura a koma Kwalejin Barewa a gani ko ya taba daukar burodin wani.
El-Rufai ya zargi Uba Sani da badakala
A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufai ya fadi yadda kuɗin kananan hukumomin Kaduna ke ɓata a mulkin Sanata Uba Sani.
Mallam El-Rufai ya yi zargin cewa Gwamna Uba Sani na canza kuɗin kananan hukumomi zuwa dalar Amurka domin ya siyan kadarori.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng