Daki da Daki: Matakan da Ake Bi a Majalisa wajen Tsige Gwamna a Najeriya
FCT, Abuja - Tsige jami’in gwamnati da aka zaɓa, kamar shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, gwamna, ko mataimakin gwamna, na nufin cire shi daga muƙaminsa ta hanyar doka kafin ƙarshen wa’adinsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Ana tsige jami'in gwamnati da aka zaɓa ne idan aka same shi da laifin cin amanar ofis ko aikata manyan laifuffuka.

Asali: Twitter
Ɓangaren majalisa ne ke da alhakin bincike da tsige waɗanda aka same su da laifin cin amanar ofis ko aikata wasu manyan laifuffuka, cewar rahoton jaridar The Nation.
Doka ta ba da damar sauke gwamna
A wasu lokuta, ana iya sauya gwamna a dalilai daban-daban kamar mutuwa, tsige shi daga muƙami, ko kuma soke zaben da ya kawo shi kan mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A Najeriya, tsarin tsige gwamna yana cikin sashe na 188 na kundin tsarin mulkin shekarar 1999, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Matakan tsige gwamna a Najeriya
Akwai matakai guda takwas da majalisar dokoki ta jiha ke bi kafin ta tsige gwamna. Ga jerinsu a ƙasa:
Mataki na 1:
Dole ne a rubuta tuhumar cin amanar ofis a kan gwamna, kuma a samu sa hannun aƙalla kashi ɗaya bisa uku (1/3) na ƴan majalisar dokokin jihar, sannan a miƙa wa kakakin majalisar dokoki ta jiha.
Mataki na 2:
A cikin kwanaki bakwai, dole ne kakakin majalisar ya aika wa gwamna da takardar tuhuma.
Mataki na 3:
Gwamna yana da haƙƙin mayar da martani kan tuhumar da ake yi masa. Dole ne a rarraba amsar gwamnan ga duk ƴan majalisar dokokin jihar.
Mataki na 4:
A cikin kwanaki 14 bayan miƙa tuhumar ga kakakin majalisa, za a kaɗa ƙuri’a domin yanke shawara kan ko a binciki gwamnan ko a’a.
Za a buƙaci akalla kashi biyu bisa uku (2/3) na dukkan ƴan majalisa su amince da shawarar ci gaba da bincike.
Mataki na 5:
Idan ƙuri’un da aka kaɗa ba su kai kashi biyu bisa uku ba, za a dakatar da shirin tsige gwamnan.
Idan aka cimma wannan kaso, kakakin majalisa zai buƙaci babban alƙalin jiha ya kafa kwamitin bincike a cikin kwanaki bakwai da amincewa da ƙudirin.
Mutanen da za su zama mambobin wannan kwamitin, dole ne su zama masu nagarta waɗanda ba su da wata alaƙa da siyasa.
Mataki na 6:
A cikin watanni uku, dole ne kwamitin ya kammala bincike sannan ya miƙa rahotonsa ga majalisar dokokin jiha.
Gwamna yana da haƙƙin kare kansa ko kuma a ba shi lauyan da zai kare shi yayin binciken.
Mataki na 7:
Idan aka kasa tabbatar da tuhumar da ake yi wa gwamnan, za a kawo ƙarshen shirin tsige shi.
Amma idan aka tabbatar da laifuffukan, majalisar dokokin jiha za ta kaɗa ƙuri’a don amincewa da rahoton binciken.
Mataki na 8:
Dole ne aƙalla kashi biyu bisa uku (2/3) na ƴan majalisar su kaɗa ƙuri’a domin amincewa da rahoton.
Idan aka amince, za a tsige gwamnan sannan a rantsar da mataimakinsa a matsayin sabon gwamna nan take.
Idan kuma tare aka tsige gwamna da mataimakinsa, shugaban majalisar dokoki zai riƙe muƙamin gwamna na wata uku, inda a cikin wannan lokacin za a yi zaɓe domin ƙarasa wa'adin gwamnan da aka tsige.
Majalisa ta fara shirin tsige Gwamna Simi Fubara
A wani labarin kuma, kun ji cewa kujerar gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ta fara yin girgiɗi bayan ƴan majalisar dokokin jihar sun taso shi a gaba.
Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin jihar ta gabatar da wasiƙar tuhume-tuhume da suka shafi saɓa doka da ake zargin Gwamna Fubara da aikatawa.
Idan shirin fara tsige gwamnan ya tabbata, zai iya rasa kujerarsa kafin tsakiyar watan Yulin 2025, domin ana ɗaukar kwanaki 120 kafin a tsige gwamna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng