Abuja: Ƙungiyoyi Sun Gudanar da Zanga Zanga, Suna So a Hukunta Wasu Alkalan Kotu
- Kungiyoyin fararen hula sun yi zanga-zanga a Abuja, suna bukatar a kawo karshen siyasantar da shari’a da kuma hukunta alkalai
- Masu zanga-zangar sun yi tattaki daga sakatariyar tarayya zuwa Kotun Daukaka Kara, suna neman “a dakatar da shari’o’in bogi”
- Shugaban masu zanga-zangar, Igwe Ude-Umanta, ya mikawa majalisar NJC jerin sunayen alkalan da suke zarginsu da cin amanar aikin su
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyoyin fararen hula sun gudanar da zanga-zangar lumana a Abuja, suna kira ga mahukunta da su kawo karshen siyasantar da shari’a a Najeriya.
Masu zanga-zangar sun rike kwalaye da rubuce-rubuce kamar haka: “A dakatar da shari’o’in bogi,” “Muna bukatar ‘yancin shari’a,” da “A hukunta alkalan da suka ci amanar shari’a.”

Asali: Twitter
Masu zanga zanga sun mika korafi ga NJC
Wasu daga cikin takardun sun kuma nuna rubuce-rubuce kamar: “Dole NJC ta dauki mataki yanzu” da “A ceci shari’ar Najeriya, lokaci ya yi,” inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zanga-zangar sun yi tattaki daga harabar sakatariyar tarayya zuwa Kotun Daukaka Kara don nuna damuwarsu kan yanke hukuncin da alakalai ke yi bisa dalilan siyasa.
Shugaban masu zanga-zangar, Kwamared Igwe Ude-Umanta, ya mika takardar korafi ga Majalisar Koli ta Shari’a (NJC) kan yadda ake amfani da shari’a don biyan bukatun siyasa.
Ya nuna damuwa kan hukuncin da aka yanke a jihohin Benuwai da Ribas, yana zargin wasu alkalai da yin hukunci da ba su dace ba.
Masu zanga-zangar sun bukaci shugabar alkalan Najeriya, Kudirat Kekereke-Ekun, da NJC da su hukunta alkalan da ake zargi da karbar cin hanci.
Ana zargin wasu alkalai da cin amanar aiki
Kungiyoyin sun yi zargin cewa babban mai shari’a na jihar Benuwai, Maurice Ikpambese, ya saba doka ta hanyar bai wa masu kara a kotun zabe rangwame ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan
Kaduna: 'Yan kasuwa sun yi zanga-zanga, sun tuna da yadda El-Rufa'i ya jawo masu matsala
Sun kuma zargi Mai shari'a Ikpambese da sauya wurin zama na kotun kararrakin zaben kananan hukumomi daga Benuwai zuwa Abuja ba bisa ka’ida ba.
Masu zanga zangar sun ce kwamishinan shari’a na Benuwai ya kai kara kotu, inda babbar kotun tarayya ta Makurdi ta hana a gudanar da shari’a a wajen Benuwai.
Sai dai sun ce a ranar 14 ga Maris, 2025, wata kotu a Abuja karkashin Mai shari'a M.M. Adamu ta bayar da umarnin a ci gaba da shari’ar a Abuja.
Masu zanga-zangar sun tambaya, ko ana iya amfani da dokar jihar Benuwai a Abuja, suna zargin Mai shari'a Adamu da cin amanar aikinsa.
An nemi Tinubu, NJC sun gyara fannin shari'a

Asali: UGC
Sun ce dole a hukunta Mai shari'a Adamu, suna mai zargin cewa ba shi da cancantar ci gaba da zama alkali a kowace kotu.
Jaridar Punch ta ce masu zanga-zangar sun yi Allah-wadai da hukuncin Kotun Koli kan rikicin majalisar jihar Ribas, wanda suka ce ya sabawa doka da tsarin shari’a.

Kara karanta wannan
El Rufai ya gamu da matsala bayan komawa SDP, ƴan kasuwa da mata sun yi masa bore
Sun kuma ce wata kwamitin alkalai mai mutum 11 karkashin Mai shari'a Mojeed Omoade ta soki yadda ake amfani da shari’a wajen biyan bukatun siyasa.
Kungiyoyin ta bukaci gwamnati da ta mutunta dokoki da ‘yancin ‘yan kasa, tana mai kiran Shugaba Bola Tinubu da kada ya yi shiru kan wannan batu.
Sun ce rikicin siyasa a Benuwai ya fi muni, domin wasu masu kara ba su ma halarci zabe ba, amma suka samu damar kai kara a gaban kotun.
Shugabar alkalai ta fito da matsalar shari'a
A wani labarin, mun ruwaito cewa, babbar mai shari’a ta jihar Kano, Dije Abdu Abdullahi, ta ce tsoma bakin sauran bangarorin gwamnati a shari’a na hana aiwatar da adalci.
Ta bayyana cewa, muddin ana barin wasu daga waje suna yin katsalandan a harkokin shari’a, to hakan zai hana lauyoyi da alkalai gudanar da aikinsu bisa gaskiya.
Asali: Legit.ng