Buhari ya bawa majalisa da bangaren shari'a ikon cin gashin kansu a bangarorin kudi

Buhari ya bawa majalisa da bangaren shari'a ikon cin gashin kansu a bangarorin kudi

Shugaba Muhammadu Buhari ya ba wa majalisa da bangaren sharia a dukkan jihohi 36 na Najeriya ikon cin gashin kansu a bangaren kudi.

Shugaban kasar ya yi hakan ne ta hanyar amfani da ikon da ya ke da shi a doka na saka hannu a kan takardar.

Shugaban kasar da ya bayyana hakan a dandalin sada zumunta na Twitter a ranar Jumaa ya kara da cewa gwamnatinsa "za ta cigaba da yin duk mai yiwuwa domin karfafa demokradiya da mulki a Najeriya."

Buhari ya bawa majalisa da bangaren shari'a ikon cin gashin kansu a bangarorin kudi
Buhari ya bawa majalisa da bangaren shari'a ikon cin gashin kansu a bangarorin kudi. Hoto daga TVC
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An kama DPO da sifetan ɗan sanda kan laifin kisan gilla a Legas

Ya rubuta, "Bisa lakari da ikon da kundin tsarin mulkin 1999 ta bani karkashin sashi na 5, Yau, na rattaba hannu kan doka mai lamba 10 na 2020 don bawa bangaren sharia da majalisun jiha ikon cin gashin kansu."

Buhari ya saka hannu kan wannan dokar ne watanni shida bayan kakakin majalisun jihohin Najeriya sun bakaci ya yi hakan.

Bayan ganawarsu da Buhari, Mudashiru Obasa, shugaban kungiyar kakakin majalisun jihohi ya shaidawa The Cable cewa suna son Buhari ya gagauta saka hannu kan dokar basu cin gashin kansu.

Duk da cewa kwaskwarimar da aka yi wa kundin tsarin mulkin shekarar 1999 ya bawa majalisun jihohin yancin cin gashin kansu a bangaren kudi, ba a aiwatar da hakan ba.

Yanzu da aka zartar da odar, hakan na nufin gwamnatin tarayya ba za ta rika danka wa gwamnonin jihohi kason kudi na majalisun jihohi ba da na bangaren sharia.

An zargi wasu gwamnoni da aka samu da laifin damfara da bannatar da kudaden da gwamnatin tarayya ke turo musu domin bawa majalisun jihohi da bangarorin sharia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel