Dalilai 8 da zai sanya Najeriya ta sanya tsarin Shari'ar Musulunci a sauran jihohi - Aanu Adegun

Dalilai 8 da zai sanya Najeriya ta sanya tsarin Shari'ar Musulunci a sauran jihohi - Aanu Adegun

A wannan rahoto, fitaccen dan jarida daga jihar Legas, Aanu Adegun, ya bayyana manyan dalilansa guda takwas da zai sanya Najeriya ta fara amfani da tsarin Shari'ar Musulunci a sauran jihohi

"Ina matukar son tsarin Shari'ar Musulunci kamar yadda naga ana amfani da ita a wasu jihohi na Arewacin Najeriya. Zancen gaskiya ma, tsarin yana daya daga cikin abubuwa mafi muhimmanci da gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo tayi.

Dalilai 8 da zai sanya Najeriya ta sanya tsarin Shari'ar Musulunci a sauran jihohi - Aanu Adegun
Dalilai 8 da zai sanya Najeriya ta sanya tsarin Shari'ar Musulunci a sauran jihohi - Aanu Adegun
Asali: Facebook

"Kafin na cigaba, bari nayi bayani akan dalilin da ya sanya Obasanjo yayi na'am da wannan tsari, hakan kuwa ya nuna cewa Obasanjo shugaba ne na gari. Haka kuma ya nuna yadda tsohon shugaban kasar ya dauki gyaran Najeriya da muhimmanci. Ya kyale kowanne gwamna ya zabi abinda yaga yafi dacewa da jama'arsa."

Ga wasu dalilai guda 8 da ya sanya nake matukar son a sanya tsarin shari'ar Musulunci a sauran jihohin Najeriya.

1. Tsarin Shari'ar Musulunci ya nuna cewa jihohin da suke amfani da shi suna da rikon addini

Maganar gaskiya, jihohin da suke amfani da tsarin Shari'ar Musulunci sunfi wadanda basa amfani da ita rikon addini. Kuma Allah zai albarkace su fiye da sauran yankuna. Ku duba sauran jihohin da suke amfani da Shari'ar Musulunci ku tabbatar da haka.

2. Tsarin Shari'ar Musulunci zai hana shugabanni satar kudin al'umma

Wani dalilin da ya sanya nake son tsarin Shari'ar Musulunci shine, shugabanni baza su samu damar satar kudin al'umma ba, saboda hukuncin da za ayi musu idan aka kama su.

3. Sanya dokar Shari'ar Musulunci zai mayar da rayukan al'umma su samu cigaba

Saboda Shari'a tana hani da abubuwa marasa kyau, kuma shugabannin wadannan wurare basa satar kudin al'umma, gwamnatin wannan wurare zata yi amfani da kudinsu wajen yin ayyukan da suka kamata.

4. Ta'addanci zai ragu a jihohin da ake amfani da shari'ar Musulunci

Kwarai kuwa abinda nace gaskiya ne. Jihohin da suke amfani da shari'ar Musulunci za a samu raguwar ta'addanci. Mai yasa? Saboda hukuncin da aka gindaya akan wanda yayi ta'addanci.

5. Ta hanyar amfani da tsarin Shari'a, jihohin zasu jefi tsuntsu biyu da dutse daya

Daya daga cikin muhimman abubuwa ga jihohin da zasu yi amfani da tsarin Shari'ar Musulunci shine, jihohin baza su yi asarar kudin shiga ba. Misali jihohin da suka hana shan giya za su samu kudin shiga daga kudin sayar da giya a jihar Legas, Anambra, Rivers, Abuja da sauransu.

6. Addini yana kawo ilimi a cikin al'umma

Wannan ba yana magana akan tsarin Shari'ar Musulunci bane kawai, addini shine babbar hanyar da ake samun ilimi. Jihohin da aka fi riko da addini sunfi cigaba.

7. Kundin tsarin mulkin Najeriya ya goyi bayan Shari'ar Musulunci

Kafin a sanya ta zama doka a wasu jihohi, ya nuna cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya goyi bayan haka, ina ganin haka ya isa a gareni.

8. Duniya tana alfahari da Najeriya a matsayin kasar dake da rikon addini

Kar ku saurari abubuwan da makiya Najeriya ke cewa. Duniya tana matukar alfahari da Najeriya a matsayin kasar dake da rikon addini.

9. Shari'ar Musulunci tana goyon bayan kare hakkin dan adam

Shari'ar Musulunci tana goyon bayan kare hakkin dan adam. A tsarin Shari'ar Musulunci akwai 'yanci ga mutum ya bayyana ra'ayinsa. A gani na wannan garabasar kada a barta wasu tsirarun jihohi kawai su more ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel