Plateau: Hankula Sun Tashi bayan Barkewar Rikicin Addini ana Cikin Azumi

Plateau: Hankula Sun Tashi bayan Barkewar Rikicin Addini ana Cikin Azumi

  • Mutanen yankin Shimankar a ƙaramar hukumar Shendam ta jihar Plateau sun samu kansu cikin tashin hankali sakamakon ɓarkewar rikici
  • Rikicin ya ɓarke ne tsakanin masu bautar addinin gargajiya da matasan Musulmi a daren ranar Lahadi, 16 ga watan Maris 2025
  • Majiyoyi sun bayyana cewa mutane da dama sun jikkata sakamakon rikicin wanda ya ci gaba har zuwa safiyar ranar Litinin
  • Hakazalika an ƙona wuraren bauta da cibiyoyin kasuwanci a dalilin rikicin wanda ya fara biyo bayan wata ƴar taƙaddama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - An samu ɓarkewar rikici a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya.

Mutane da dama sun jikkata yayin da aka ƙona gidaje sakamakon saɓanin da ya faru tsakanin masu bautar addinin gargajiya da matasan Musulmi.

Rikici ya barke a Plateau
Mutane sun jikkata sakamakon barkewar rikici a Plateau Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Facebook

Rikici ya ɓarke a jihar Plateau

Kara karanta wannan

Araha kamar gidan biki: Gwamnatin Sokoto ta dauki matakin karya farashin kayan abinci

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rikicin ya auku ne a yankin Shimankar da ke ƙaramar hukumar Shendam ta jihar Plateau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bankawa wuraren bauta na addini da cibiyoyin kasuwanci wuta sakamakon ɓarkewar rikicin, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa tashin hankalin, wanda ya fara a daren Lahadi, ya ci gaba har zuwa safiyar Litinin, duk da isowar ƴan sanda da sojoji, wanda hakan bai hana lamarin yin ƙamari ba.

Majiyoyin sun ce rikicin ya samo asali ne lokacin da masu bautar gargajiya ke wucewa, sai wata taƙaddama ta taso tsakaninsu da wasu matasan Musulmi, wanda daga nan ya rikiɗe zuwa tashin hankali.

Ƴan sanda ba su ce komai ba

Mai magana da yawun bakin ƴan sandan jihar Plateau, DSP Alabo Alfred, bai dawo da amsar tambayoyin da aka yi masa kan lamarin ba.

Sai dai, Manjo Samson Zhakom, mai magana da yawun rundunar Operation Safe Haven (OPSH), rundunar haɗin gwiwa da ke kula da tsaro a jihar Plateau, ya tabbatar da cewa zai tuntuɓi hukumomin da abin ya shafa kan batun.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza fada da 'yan bindiga, sun hallaka miyagu a Zamfara

Mazauna yankin sun bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da tashin hankali, kuma sun yi kira da a tura jami’an tsaro don shawo kan lamarin.

A jihar Plateau dai a kan yawan samun rikice-rikicen addini da na ƙabilanci lokaci bayan lokaci.

Jihar dai tana da ƙabilu da dama tare da mabiya addinai daba-daban. Rikice-rikicen su kan haifar da asarar rayuka tare da tarin dukiya mai yawa.

Musulmai da Kirista sun rungumi zaman lafiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa al'ummar Musulmi da Kirista a garin Gangare na ƙaramar hukumar Jos ta Arewa sun rungumi zaman lafiya da juna.

Mazauna garin na Gangare sun koma matsunansu bayan rikicin addinin da ya ɓarke a Jos a shekarar 2001 wanda ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane masu yawa.

Bayan aukuwar rikicin dai, an samu rarrabuwar kai tsakanin al'ummar Musulmi da Kirista na garin inda suka ƙauracewa juna.

Kara karanta wannan

Yunkurin tsige gwamna ya jefa Shugaba Tinubu a matsala, an yi masa barazana

Sai dai, komai ya zo ƙarshe bayan mazauna garin sun yanke shawarar rungumar juna domin su ci gaba da zama tare a matsayin ƴan uwan juna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng