'Yan Ta'adda Sun Kai Hari Ribas, Sun Ƙona Gidan Ministan Abuja? Bayanai Sun Fito
- Rundunar ‘yan sanda ta Rivers ta karyata rahotannin da ke cewa ‘yan ta’adda sun kai hari tare da kona gidan ministan Abuja, Nyesom Wike.
- SP Grace Iringe-Koko ta bayyana cewa ba a samu wani rahoto kan harin ba, tana mai cewa labarin kirkirarre ne don haddasa tashin hankali.
- Rundunar ‘yan sanda ta yi gargadi kan yada labaran karya, tana mai cewa za a dauki matakin doka kan duk wanda aka kama a tada fitina.
- Ta tabbatar wa jama’a da cewa zaman lafiya na ci gaba da wanzuwa, tare da bukatar su kai rahoton duk wani motsi da suke zargi ga hukumomin tsaro.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ribas - Rundunar 'yan sandan jihar Rivers ta karyata rahotannin da ke cewa wasu ‘yan ta'adda sun kai hari tare da kona gidan ministan Abuja, Nyesom Wike.
A daren Lahadi, wasu kafafen yada labarai na intanet suka wallafa cewa an kai farmaki kan gidan Nyesom Wike da ke Fatakwal, har ma aka cinna masa wuta.

Asali: Facebook
'Yan sanda sun karyata kona gidan Wike
Sai dai, a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, kakakin ‘yan sandan jihar, SP Grace Iringe-Koko, ta ce wannan rahoto ba gaskiya ba ne, inji Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
SP Grace ta ce rundunar ta lura da wata jita-jita mai nasaba da rikicin Rivers, tare da ikirarin cewa an kona gidan tsohon gwamna Nyesom Wike.
Ta bayyana cewa ba a samu wani rahoto na irin wannan hari ba, tana mai cewa labarin karya ne da aka kitsa domin haifar da tashin hankali.
'Yan sanda sun aika sako ga mazauna Ribas
Kakakin rundunar ta bayyana cewa:
"Rundunar 'yan sanda na bayyana cewa wannan rahoto ba gaskiya ba ne, kuma an kirkire shi ne domin haifar da rudani da firgitar da jama’a"
SP Grace ta yi kira ga al’umma da su yi watsi da wadannan rahotanni marasa tushe, tana mai tabbatar da cewa zaman lafiya na ci gaba da wanzuwa a jihar.
Kakakin rundunar ta gargadi masu yada labaran bogi da su daina aikata abin da ka iya haifar da tashin hankali ko rikici a jihar.
Ribas: Za a hukunta masu yada jita-jita

Asali: Twitter
SP Grace ta ce:
"Za a dauki matakin doka kan duk wanda aka kama yana yada labaran karya ko kokarin haddasa fitina da kawo cikas ga zaman lafiya."
Ta tabbatar wa jama’a da cewa rundunar tana aiki tukuru domin tabbatar da tsaro, tare da shawartarsu da su dogara da ingantattun hanyoyin samun labarai.
Ta kuma bukaci mazauna jihar da su rika kai rahoton duk wani motsi da suke zargi ga hukumomin tsaro don daukar matakin da ya dace.
An cafke matasa a kusa da gidan Wike
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an tsaro sun kama wasu matasa tare da gurfanar da su a kotu bisa zargin haddasa hargitsi a kusa da gidan Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Matasan da suka hada da Nasiru Abdullahi, Usman Jibrin, da Aliyu Adamu, an cafke su bisa hayaniyar da ta tayar da hankalin jama’a a yankin.
Dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Godwin Gabriel, ya shaidawa kotu cewa an yi wa matasan gargaɗi tun farko, amma suka ki bin umarni.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng