Zargin Lalata: Ana Shirin Cafke Sanata Natasha kan Jawabin da Ta Yi a Taron IPU? Bayanai Sun Fito

Zargin Lalata: Ana Shirin Cafke Sanata Natasha kan Jawabin da Ta Yi a Taron IPU? Bayanai Sun Fito

  • Majalisar Dattawa ta musanta zargin shirya kama dakatacciyar sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan da zaran ta dawo Najeriya
  • Mai magana da yawun Majalisar, Sanata Adeyemi Adaramodu ya ce da alama Sanata Natasha ta fara gane illar abin da ta yi a taron IPU ne
  • Natasha ta kai ƙorafin shugaban Majalisar Dattawa gaban Majalisar Ɗinkin Duniya kuma ta yi zargin ana shirin kamata ida ta dawo Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Majalisar Dattawan Najeriya ta musanta ikirarin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ‘yar majalisa mai wakiltar Kogi ta Tsakiya da aka dakatar, ta yi.

Tun farko dai dakatacciyar sanar ta yi zargin cewa ana shirin kama ta da zarar ta dawo daga taron IPU na Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar a birnin New York na ƙasar Amurka.

Kara karanta wannan

"Gwamnatin Najeriya na shirin kama ni": Sanata Natasha ta fadi halin da take ciki

Majalisar Dattawa.
Majalisar Dattawa ta musanta zargin Natasha Akpoti-Uduaghan kan shirin kama ta Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Majalisar Dattawan Najeriya ta musanta wannan zargi na kama Natasha, tana mai cewa babu kanshin gaskiya a ciki, kamar yadda Leadership ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da gaske ana shirin kama Natasha?

Mai magana da yawun majalisar, Sanata Adeyemi Adaramodu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 17 ga watan Maris, 2025.

Ya ce babu wata hujja ko dalilin da zai sanya Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da majalisar gaba ɗaya su shiga cikin lamarin.

Adeyemi Adaramodu ya ce:

"Shugaban Majalisar Dattawa da Majalisar Dattawan Najeriya ba su da dalilin tsoma kansu cikin wannan batu.”

Sanata Natasha ta zargi gwamnatin Tinubu

A ranar Lahadi, Sanata Natasha ta yi zargin cewa gwamnati na shirya yadda za a kama ta da zarar ta iso Abuja daga Amurka.

“Ina da tabbacin cewa ana shirin kama ni da zarar na dawo babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Natasha: Kungiyar 'yan majalisun duniya ta karbi koken Sanata, za ta ji ta bakin Akpabio

"Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya tura wasu jami’ai guda uku, ta ofishin jakadancin Najeriya da ke New York, don su fitar da ni daga ɗakin taron Majalisar Ɗinkin Duniya jim kaɗan bayan na gabatar da jawabi.
“Daga baya ‘yan majalisa daga wasu ƙasashe duniya da jami’an tsaro suka kubutar da ni.”

- Cewar Sanata Natasha.

Sanatar ta kuma jaddada cewa halartar taron IPU na ƴan Majalisun ƙasashen Duniya, da ta yi bai saɓa doka ba, duk da dakatar da ita da majalisar dattawa ta yi.

Sanata Natasha.
Sanata Natasha ta fara zargin Majalisa na shirin sa a kama ta a Abuja Hoto: Natasha H. Akpoti
Asali: Facebook

Majalisar Dattawa ta mayar da martani

Da yake mayar da martani, Sanata Adaramodu ya bayyana cewa Natasha Akpoti-Uduaghan fa fara ganin illla da sakamakon abin da ta aikata a taron IPU.

“In dai jin tana tsoron sakamakon maganganu marasa kima da ta yi kan Najeriya a taron IPU a New York, to ya kamata ta daina jefa laifin kan majalisar dattawa domin ba ruwanta da wannan hanya maras kyau da ta ɗauko.

Kara karanta wannan

Sanata Natasha ta kai karar Akpabio ga kungiyar 'yan majalisun duniya

- Sanata Adeyemi Adaramodu.

DSS da NIA sun taso sanata Natasha

A wani labarin, kun ji cewa hukumomin DSS da NIA sun fara gudanar da bincike kan yadda Natasha ya samu damar halartar taron kungiyar ƴan Majalisun duniya (IPU).

Rahoto ya bayyana cewa manyan hukumomin tsaron Najeriya na gudanar da bincike ne don gano wanda ya ba sanatar damar shiga taron da aka yi a Amurka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel