Lokacin Matasa Ya Yi: Atiku Ya Yaba da Yadda Matashiya ’Yar Bautar Kasa Ta Soki Tinubu

Lokacin Matasa Ya Yi: Atiku Ya Yaba da Yadda Matashiya ’Yar Bautar Kasa Ta Soki Tinubu

  • ‘Yan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin baki kan yadda wata matashiya ke sukar gwamnati a sansanin NYSC, har ta samu matsala da hukuma
  • Atiku Abubakar na daga cikin wadanda suka ba ta kwarin gwiwar tabbatar da an samu sauyi mai dorewa a Najeriya, musamman a yanayin da ake ciki
  • Ya bayyana cewa, matasa irin Raye ne ke tashi domin tabbatar da an samu sauyi a fannin siyasa da ci gaban kasa mai girma irin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Najeriya - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya yabawa wata matashiya ‘yar gwagwarmaya, Raye, bisa jajircewarta a fagen a kare muradun al’umma.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter (X), Atiku ya bayyana Raye a matsayin misali na sabon karnin mata masu rajin kawo sauyi da adalci a cikin al’umma.

Kara karanta wannan

An yi ca kan NYSC bayan barazana ga mai bautar ƙasa da ta soki gwamnatin Tinubu

Ya ce matashiyar ta nuna kwazon da ke karfafa gwiwar matasa, kuma tana da karsashi da hikimar da za ta iya jagorantar sauyi a Najeriya.

Matashiya ta sha yabo daga Atiki bayan sukar Tinubu
Atiku ya yabawa matashiya Raye kan sukar Tinubu | Hoto: @Atiku/@AmnestyNigeria/Asiwaju
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Raye ta cancanci girmamawa, inji Atiku

Atiku ya yaba da irin karsashin da Raye ke da shi, yana mai cewa tana da karfin hali da jajircewa wajen bayyana gaskiya ba tare da tsoro ba.

A cewarsa, irin wannan jajircewa da tsayin daka yana nuna cewa matasan Najeriya sun shirya don daukar nauyin jagoranci a nan gaba.

Ya ce shugabanni su daina ganin matasa ‘yan gwagwarmaya a matsayin abokan gaba, maimakon haka, a basu dama da goyon baya domin ci gaba da fafutuka don inganta rayuwar al’umma.

Ta bi sawun manyan jaruman mata a Najeriya

Atiku ya kwatanta Raye da wasu daga cikin fitattun matan da suka fafata don neman adalci da ci gaban Najeriya, irin su Gambo Sawaba, Funmilayo Ransom-Kuti, da Margaret Ekpo.

Wadannan mata sun kasance ginshikai a tarihin gwagwarmayar kare hakkin al’umma, kuma sun taka rawar gani wajen tabbatar da cewa mata sun samu damar shiga siyasa da sauran al’amuran zamantakewa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaban Amurka, Trump ya samu izinin kakaba takunkumi ga Najeriya

A cewarsa, irin su Raye suna bin sahun wadannan jaruman, suna cigaba da tabbatar da cewa an baiwa kowa dama, musamman mata da matasa.

Shugabannin gobe sun riga sun bayyana, cewar Atiku

Atiku ya jaddada cewa lokacin matasa ya yi, kuma shugabannin gobe sun riga sun fara bayyana a cikin al’umma.

Ya ce matasa su ci gaba da jajircewa, su guji karaya, domin makomar Najeriya tana hannunsu.

A cewarsa:

"Raye ta zama misalin yadda matasa ke kokarin sauya al’amura. Ita ce wakiliyar sabon karni na jagorori da za su gina makomar kasa."

Ya ce idan aka baiwa irin su Raye dama, Najeriya za ta ga sauyin da ake fata, domin matasan da ke da hangen nesa su ne makoma mai haske ga kasa.

Akwai bukatar goyon baya ga matasa, Atiku

Atiku ya bukaci shugabanni da su daina tauye damar matasa masu rajin kawo canji a Najeriya.

A cewarsa, irin su Raye ba su cancanci a muzguna musu ko a hana su magana ba, sai dai ma a ba su dama da goyon baya.

Kara karanta wannan

'Farashin abinci da fetur ya sauka a Najeriya': Minista ya zayyano alheran Tinubu

Ya kara da cewa, idan ana son ci gaban kasa, to matasa su samu cikakken damar jagoranci da sauya fasalin al’amura.

Kalaman karfafa gwiwa daga Atiku ga matasa

Kalaman Atiku na zuwa ne a lokacin da matasa ke kara tashi tsaye domin ganin an inganta rayuwar ‘yan kasa.

A baya, an ga matasa kamar su Aisha Yesufu, Rinu Oduala, da Omoyele Sowore suna jagorantar gwagwarma mai tasiri don kawo canji.

A yanzu, ana ganin cewa irin wannan goyon baya daga jiga-jigan siyasa zai kara wa matasa kwarin gwiwa don cigaba da fafutuka.

Yadda batun Raye ya faro

Idan baku manta ba, matashiya Raye ta yada bidiyon a kafar sada zumunta, inda ta ce ana mata barazana a sansanin NYSC kan sukar gwamnatin Tinubu.

Ya bayyana kukanta ne kan yadda ‘yan Najeriya kef ama da tsadar rayuwa a karkashin mulkin APC ta Bola Ahmad Tinubu.

Ya kuma bayyana damuwa kan yadda aka bukaci da goge bidiyon da ta daura kan sukar gwamnati da ta yi daga wani jami’in hukumar NYSC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

iiq_pixel