'Ka Nemi Afuwa': Gidauniyar Dahiru Bauchi ga El Rufai, Ta ba Shi Wa'adi kafin Ƙarshen Ramadan
- Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi ta bukaci Nasir El-Rufai ya nemi afuwa bisa zargin rashin adalci da kuma tsangwamar ɗalibai
- Gidauniyar ta fitar da takarda da Sayyadi Aliyu ya sanya wa hannu, tana buƙatar El-Rufai ya amsa laifi da neman gafara
- Ana zargin tsohon gwamnan ya umarci jami’an tsaro su kai samame a makarantu da kama ɗaliban Alƙur’ani
- Gidauniyar ta ce za ta kai kara gaban kotu ko shugaban kasa idan har ba a nemi afuwa ba kafin ƙarshen Ramadan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ta gargadi tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
Gidauniyar ta bukaci Nasir El-Rufai, da ya nemi afuwa bisa wasu laifuka da ta zarge shi kafin karshen watan Ramadan.

Asali: Facebook
An yi zanga-zangar kin jinin El-Rufai a Kaduna

Kara karanta wannan
El Rufai ya gamu da matsala bayan komawa SDP, ƴan kasuwa da mata sun yi masa bore
Takardar ta samu sa hannun Sayyadi Aliyu Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, inda aka nemi El-Rufai ya yarda da laifi tare da neman gafara, kamar yadda Gidauniyar ta wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanann na zuwa ne yayin wasu mutane suka fito zanga-zanga a Kaduna domin nuna rashin jin dadi a mulkin tsohon gwamnan.
Yan kasuwa da ƙungiyoyin mata sun gudanar da zanga-zanga a Kaduna, suna nuna goyon baya ga Gwamna Uba Sani da Shugaba Bola Tinubu.
Sun gudanar da wannan zanga-zangar ne 'yan kwanaki bayan ficewar El-Rufai daga APC zuwa SDP, inda suka ce ba za su yarda a yaudare su ba.
Zargin da ake yi wa El-Rufai a Kaduna
A cewar gidauniyar, El-Rufai ya aikata rashin adalci ga ɗalibai da jagoransu, Sheikh Ɗahiru Bauchi, ta hanyar umarnin kai samame a makarantunsu.
Sanarwar ta ce:
"Idan kuwa bai yi hakan ba kafin ƙarshen watan Ramadan, za mu maka shi a kotu."

Asali: Twitter
Ana ci gaba da neman dalibai da suka bace
Gidauniyar ta zargi tsohon gwamnan da umartar jami’an tsaro su kai samame a tsangayar Sheikh, inda aka kama ɗaliban Alƙur’ani.
Rahoton ya nuna cewa wasu daga cikin ɗaliban da aka kama har yanzu ba a san inda suke ba, lamarin da ya jawo damuwa.
Sayyadi Aliyu ya bayyana cewa hakan na da nufin tozarta Sheikh Ɗahiru Bauchi da hana ci gaban addinin Musulunci da ya ke koyarwa.
Ya ce:
"Idan har El-Rufai bai nemi afuwa ba kafin ƙarshen Ramadan, za mu kai kararsa gaban Shugaban Ƙasa da kungiyoyin kare haƙƙi."
Gidauniyar ta kuma yi barazanar kai ƙarar gaban kotu, kuma idan hakan ya ci tura, za su ɗora lamarin ga Allah ta hanyar addu'a.
Sule Lamido ya soki El-Rufai kan kiran shiga SDP
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya soki Nasir El-Rufai inda ya ce ba ya da darajar shugabanci, ba zai iya janyo ‘yan PDP su bi shi SDP ba.

Kara karanta wannan
"Ba mu yarda ba," El Rufai ya ƙara shiga matsala bayan komawa SDP, matasa sun masa rubdugu
Tsohon gwamnan ya ce El-Rufai bai cancanci gayyatar manyan ‘yan adawa zuwa sabuwar jam’iyyarsa ba domin ba shi da kishin kasa da nagarta .
Lamido ya kara da cewa PDP ce ta haifi El-Rufai, bai kamata ya koma baya ya soke jam’iyyar da ta dauke shi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng