'Yan Jagaliya Aka Tara': Obasanjo Ya Fadi Halayen Sarakuna da Ake Nadawa a Yanzu

'Yan Jagaliya Aka Tara': Obasanjo Ya Fadi Halayen Sarakuna da Ake Nadawa a Yanzu

  • Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya koka kan yadda 'yan ta'adda da masu shaye-shaye ke zama sarakuna a Najeriya
  • Obasanjo ya ce yawancin sarakunan yanzu ba su da tarbiyya ko horo, kuma hakan na lalata darajar sarauta
  • Ya bayyana cewa wasu sarakuna ma na aikata ba daidai ba kamar satar akwatin zaɓe yayin zaɓe
  • Tsohon shugaban ya bukaci a mayar da daraja da mutuncin sarauta domin ci gaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya nuna damuwa game da yadda ake zabar sarakuna, yana cewa 'yan ta’adda da masu laifi sun mamaye masarautu.

Obasanjo ya ce yawan yaduwar sababbin sarakuna da rashin tarbiyya da horo ya haddasa tabarbarewar tsarin gargajiya a fadin kasar nan.

Obasanjo ya nuna damuwa kan irin sarakuna da ake nadawa yanzu
Olusegun Obasanjo ya ce sarakuna da ake nadawa yanzu ba su tarbiyya. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Obasanjo ya koka kan tarbiyar sarakunan yanzu

Kara karanta wannan

Bayan taimakon Nijar, Najeriya ta fadi haɗarin da ke tunkaro ta daga makwabtanta

Obasanjo ya bayyana hakan ne a cikin sabon littafinsa 'Nigeria: Past and Future' wanda aka kaddamar a makon da ya gabata, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban ya koka da cewa an bar tsarin horo da koyarwar gargajiya da ke kare mutuncin sarauta, wanda hakan ke kara wa matsaloli tsanani.

Ya ce,

“Yau akwai 'yan ta’adda, masu shaye-shaye, ’yan daba da masu garkuwa da mutane a matsayin sarakuna.”
Obasanjo ya bukaci ba sarakuna horo da tarbiyya
Olusegun Obasanjo ya ce mafi yawan sarakuna da ake nadawa ba su da tarbiyya. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Obasanjo ya ce akwai sarkin da ya sace akwatin zabe

Obasanjo ya kara da cewa wasu sarakuna ba sa kiyaye al’adu da adalci, maimakon haka suna aikata abubuwan kunya da ke lalata tsarin kasa.

Ya kawo misalin wani sarki da ya saci akwatin zaɓe a rumfar kada kuri’a kuma ya tsere da shi.

Ya tuna lokacin da sarakuna ke da daraja da girmamawa a lokacin mulkin mallaka da farkon bayan samun ’yancin kai.

Ya ce:

“Ina nufin irin sarakunan da ke da mutunci da daraja kamar yadda muka san su a zamanin da, yanzu an yi musu lahani.”

Kara karanta wannan

Al-Mustapha ya ziyarci Atiku awanni da sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP

“Wannan mutunci da daraja ya kamata a dawo da su. Sarakuna su zama abin alfahari ga ci gaban Najeriya."

Obasanjo ya bukaci a gaggauta gyara tsarin sarauta domin dawo da mutuncin da aka rasa a kasar nan.

Ya ce sarakuna ya kamata su zama ginshikin ci gaban kasa, ba wani nauyi da ke hana ci gaba ba.

Obasanjo ya jaddada bukatar dawo da dabi’u na gari musamman tsakanin sarakunan da ke da tarihi da tushe.

Ya ce idan aka gyara su yadda ya kamata, za su taka rawa sosai wajen cimma burin Najeriya mai nagarta.

“Akwai bukatar dawo da tarbiyya tsakanin sarakuna musamman na gargajiya, za su iya taimakawa wajen gina Najeriya da muke mafarki.”

- Cewar Obasanjo

El-Rufai ya magantu kan rigimar Atiku, Obasanjo

Mun ba ku labarin cewa Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya ce Olusegun Obasanjo ya fi gaskiya a rikicinsa da Atiku Abubakar.

El-Rufai ya ce ba siyasa ba ce ta haifar da goyon bayansa ga Obasanjo, ya ce babu wata rashin jituwa tsakaninsa da Atiku Abubakar kamar yadda akae yadawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel