Iyalan Abba Kyari Sun Ƙaryata Zargin Samun N200m, Sun Fadi Kudin da Ya Mallaka
- Iyalan Abba Kyari sun karyata zargin yana da asusun banki guda 10 da N200m, inda suka ce labarin karya ne da aka shirya
- Sun bayyana cewa yana da asusu a bankuna hudu kawai da jimillar kudin da bai kai N4m ba kacal
- Shaida a kotu ya tabbatar babu wata alaka tsakanin kudin asusun Kyari da wata haramtacciyar hulɗa ko laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja – Iyalan tsohon mataimakin kwamishinan yan sanda, Abba Kyari sun yi magana kan zarge-zargen da ake yi masa.
Iyalan tsohon Shugaban IRT, sun karyata rahoton cewa yana da asusun banki 10 da N200m a cikinsa.

Asali: Twitter
Wane martani iyalan Kyari suka yi?
Rahoton ya fito ne yayin ci gaba da sauraron karar bayyana kadarori da aka yi a ranar 13 ga Maris, 2025, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cikin wata sanarwa, Daniel Okpotu, mai taimaka wa iyalin Kyari a harkokin yada labarai, ya bayyana cewa Kyari na da asusu a bankuna hudu kacal.
Har ila yau, an bayyana cewa dukkan kudaden shiga da fita cikin shekaru 23 sun kai N200m ciki har da albashi da wasu halattattun kudade.
Yayin tambayoyi a gaban kotu, wani shaida daga bangaren masu kara ya tabbatar babu wata alaka tsakanin kudin da wani laifi.
Iyalan Abba Kyari sun zargi wasu mutane da yunkurin yada irin wadannan labarai na karya tun shekaru uku da suka wuce.

Asali: Facebook
Iya adadin kudi da Kyari ya taba rikewa
Sanarwar ta bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da rahotannin da ba su da tushe, suna cewa Kyari bai taba rike fiye da N5m ba.
An saurari karar ne a gaban kotu a bainar jama’a, lamarin da ya ja hankalin mutane saboda zargin shari’ar kafafen watsa labarai.
Iyalan sun jaddada cewa kowanne ma’aikacin banki a Najeriya zai iya tabbatar da gaskiyar bayanan kudin Kyari.
Sanarwar ta ce:
“Rahoton cewa Abba Kyari yana da asusun banki 10 da N200m karya ne kuma an shirya shi don karkatar da al’amura.
“Gaskiyar magana, wacce kowanne ma’aikacin banki zai iya tabbatarwa, ita ce Kyari na da asusu a UBA, GTB, Sterling da Access, ba fiye da haka ba.
Wani shaida ya tabbatar babu wata hujja da ke nuna kudin na da nasaba da wani laifi inda ya ce wadannan wasu irin karairayin da aka yada shekaru uku da suka wuce ne.
“Mun halarci kotu a ranar Laraba; a fili ne aka saurari shari’ar. Abin mamaki ne yadda ake yada karairayi ba tare da hujja ba.
“Abba Kyari bai taba rike N5m a kowanne asusu cikin shekaru goma da suka wuce ba, yan Najeriya kada su yarda da wannan labarin karya.”

Kara karanta wannan
An sake rikita Tinubu, Kwankwaso, Obi da gwamnonin PDP sun shirya raba shi da mulki
Cewar sanarwar
An ba da belin Abba Kyari
A baya, kun ji cewa an sake tsohon dan sanda, DCP Abba Kyari daga gidan gyaran hali bayan shafe watanni 27 a kulle a birnin Abuja.
Rahotanni sun ce an sake Kyari ne bayan ya cika duka ka'idojin ba da beli da ake bukata daga gare shi kamar yadda hukumomi suka tabbatar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng