Katsina: Sojojin Sama Sun Ragargaji 'Yan Bindiga, Sun Hallaka Miyagu Masu Yawa
- Dakarun sojojin sama sun samu nasarar da za a yi ta magana a kan ta kan ƴan bindigan da ke kai hare-hare a jihar Katsina
- Sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun kai farmaki a kan maɓoyar ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar
- Jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga 19, ciki har da wasu manyan jagororinsu guda biyu a yayin farmakin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Dakarun sojojin sama da ke ƙarƙashin rundunar Operation Fansa Yamma sun kai gagarumin farmaki kan ƴan bindiga a jihar Katsina.
Dakarun sojojin sun kai farmakin ne kan maɓoyar ƴan bindiga a dajin Unguwar Goga, da ke yankin Ruwan Godiya, a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Asali: Getty Images
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Ana daf da cafke hatsabibin ɗan bindiga da ake nema ruwa a jallo bayan kama hadiminsa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojoji suka farmaki ƴan bindiga
Majiyoyi sun bayyana cewa dakarun sojojin sun kai farmakin daga safiyar ranar 13 ga watan Maris zuwa tsakar rana.
Farmakin ya yi sanadiyyar rushe wasu manyan sansanoni biyu na shugabannin ƴan bindiga da aka daɗe ana nema kamar Gero (Alhaji) da Alhaji Riga.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa aƙalla ƴan bindiga 19 ne aka kashe yayin harin, yayin da alamu suka nuna cewa wasu da dama sun mutu a cikin duwatsun yankin, amma har yanzu ba a tantance adadinsu ba.
Binciken bayan harin ya nuna cewa Alhaji Riga da Gero su ne ke ba da mafaka ga wasu manyan ƴan ta’adda da suka daɗe suna addabar jama’a.
Ƴan ta'addan sun daɗe suna haddasa hare-hare a yankin hanyar Funtua-Gusau, musamman tsakanin ƙauyukan Yankara da Sheme.
Jami’an tsaro na ci gaba da sintirin sama da ƙasa domin bibiyar ƴan bindigan da suka tsere tare da hana su sake haɗuwa da juna domin cigaba da ayyukan ta’addanci.
Sojoji sun taso ƴan bindiga a gaba
Rundunar sojojin Najeriya ta tsananta farmaki a yankin Arewa maso Yamma, inda take kai hare-hare a sansanonin ƴan bindiga tare da katse hanyoyin samun makamai da kayan abinci, domin dawo da zaman lafiya a yankin.
An bayyana cewa sojojin za su ci gaba da kai hare-hare da kuma amfani da dabarun yaƙi domin murƙushe ragowar ƴan ta’addan da suka rage, tare da tabbatar da cewa ba su samu damar sake kafa wasu sansanonin ba.
Wannan farmaki na daga cikin yunƙurin gwamnati na daƙile ayyukan ƴan bindiga da kuma tabbatar da cewa jama’a sun komawa rayuwarsu ta yau da kullum ba tare da fargaba ba.
Sojojin sama sun hallaka ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sama na Najeriya sun samu nasarar yin luguden wuta kan ƴan bindiga a jihar Neja.
Dakarun sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun hallaka ƴan bindiga da dama a yayin harin da suka kai, a maɓoyarsu da ke dajin Alawa cikin ƙaramar hukumar Shiroro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng