Rigimar Sarauta Ta Dawo, Kotu Ta Yi Hukunci kan Mayar da Sanusi II Kujerarsa
- Kotun daukaka kara a Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncinta na 10 ga Janairun 2025 kan soke dokar masarautar Kano
- Kotun ta ce hukuncin Mai Shari'a, Abubakar Liman wanda ya soke matakan gwamnatin Kano ba da hurumi ya yi ba ne
- Mai shari'a, Okon Abang ya ce dole ne a tsaya kan matsayin da ake kafin hukuncin kotun tarayya da za a saurari kotun koli
- Kotun daukaka karar ta umarci masu kara su dakatar da aiwatar da hukunci har sai kotun koli ta yanke hukunci na karshe
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - A wani sabon salo a rikicin masarautar Kano, Kotun Daukaka Kara a Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncinta na 10 ga Janairu.
Hukuncin ya amince da soke dokar 2019 ta kafa sabbin masarautu, amma kotun ta dakatar da shi har sai kotun koli ta yanke hukunci.

Kara karanta wannan
Aminu vs Sanusi II: An bayyana sahihin sarkin Kano bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara

Asali: UGC
Wane umarni kotu ta bayan kan sarautar Kano?
Kotun Daukaka Kara a Kano ta soke umarnin da Mai Shari'a, Abubakar Liman ya bayar a ranar 20 ga Yunin 2024 kan dokar rushe masarautun 2024, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta ce babu hurumin Mai Shari'a Liman ya soke matakan da gwamnatin Kano ta dauka bisa dokar da aka amince da ita a 2024.
Bayan rashin jin dadin hukuncin, gwamnatin Kano ta daukaka kara zuwa kotun koli tare da neman dakatar da aiwatar da hukuncin.
Hukuncin yau Juma’a ya fito ne daga kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin Justice Okon Abang, a karar da Aminu Babba Dan ya shigar.
Aminu Baba Dan (Sarkin Dawaki Babba), ya shigar da karar tun 6 ga Fabrairun 2025 yana neman kotu ta dakatar da aiwatar da hukuncin.
Mai kara ya ce dokar 2024 da gwamnatin Kano ta zartar ita ta rushe sababbin masarautu kuma ta dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki.

Asali: Twitter
Kotu ta dakatar da hukuncin da ta yanke a baya
Alkalai ukun karkashin Mai Shari'a, Abang sun yanke hukunci tare da bayyana cewa bukatar da aka gabatar tana da tushe kuma ta cancanci amincewa.
Mai shari'a, Abang ya ce:
“Dokar kotu ta tabbatar da cewa za a yi amfani da ikon kotu cikin adalci da gaskiya don tabbatar da shari’a.”.
Ya kara da cewa akwai matakin daukaka kara a gaban kotun koli, kuma dole ne a kare batun da ake shari’a a kansa, cewar Vanguard.
Kotun ta hana gwamnati aiwatar da hukuncin ranar 10 ga Janairun 2025 wanda ya soke rushen sabbin masarautu da dawo da Sarki Sanusi II.
Ta kuma bayar da umarnin cewa a ci gaba da zama kan matsayin da ake har sai kotun koli ta fitar da hukunci na karshe.
Hukuncin kotun daukaka kara na 10 ga Janairu ya soke na babbar kotun tarayya da ta bayyana dokar rushe masarautu a 2024 a matsayin mara inganci.
Kotun daukaka kara ta bayyana cewa kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron batun masarauta wanda ya rage ga kotun jiha kawai.
Jami'an tsaro sun tushe kofar Nasarawa
Kun ji cewa dakarun ƴan sanda da sauran jami'an tsaro sun tsaurara matakan tsaro a titin zuwa fadar Nasarawa, wurin da sarki na 15, Aminu Ado Bayero yake zaune.
Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaron sun toshe dukkan hanyoyin da ke kai wa zuwa ƙaramar fadar Nasarawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng