'Yan Boko Haram Sun Kai Harin Ta'addanci a Yobe, Sun Tafka Barna
- Wasu ƴan ta'addan Boko Haram sun kai harin ta'addanci a jihar Yobe da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
- Ƴan ta'addan sun kai harin ne cikin dare a garin Gujba da ke ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe
- Miyagun sun hallaka wani ɗan sa-kai mai shekara 32 a duniya tare da ƙona daƙuna da gidaje masu yawa a yayin harin
- Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya jajantawa mutanen da harin ya shafa, ya ba su tabbacin cewa gwamnatinsa za ta tallafa musu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Yobe - Wasu da ake zargin ƴan ta'addan Boko Haram ne sun kashe wani ɗan sa-kai mai suna Modu Bulama mai shekaru 32 a jihar Yobe.
Ƴan ta'addan na Boko Haram sun kuma lalata ɗakuna 12 da shaguna takwas a harin da suka kai a garin Gujba na jihar.

Asali: Original
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa majiyoyi sun ce maharan sun afka garin Gujba da ke ƙaramar hukumar Gujba a daren ranar Asabar yayin da mazauna yankin ke barci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ƴan ta’addan sun bi gida-gida suna nemam ƴan sa-kai kafin su kashe Modu Bulama yayin da yake ƙoƙarin tserewa.
Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Yobe (SEMA), Dr. Goje Muhammad, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Goje Muhammad ya bayyana cewa hukumar ta gudanar da bincike tare da miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan Bulama da sauran waɗanda abin ya shafa.
“Bincikenmu ya gano cewa gidaje 14, da ke ɗauke da kimanin mutum 57, harin ya shafa kai tsaye."
"Jimillar ɗakuna 12 da shaguna takwas waɗanda mafi yawansu na ƴan kasuwa da ƴan sa-kai ne, sun ƙone kurmus."
“Abin takaici, wani ɗan sa-kai mai shekaru 32 ya rasa ransa, ya bar mata biyu da ƴaƴa bakwai."
Gwamna Mai Mala Buni ya jajantawa waɗanda lamarin ya shafa, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnati za ta tallafa musu da kuma ƙara matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.
Hare-haren Boko Haram a Gujba
Wannan ba shi ne karo na farko da ƴan ta'addan Boko Haram suka kai hari a garin Gujba ba.
A watan Janairu na wannan shekarar, ƴan ta’addan sun kai hari a yankin, inda suka yi awon gaba da mota ƙirar Toyota Hilux mallakar ƴan sa-kai.
Sojoji sun nuna bajinta kan 'Yan Boko Haram
Kwanakin baya rahoto ya gabata cewa wani babban mai haɗa bama-bamai ga ƴan ta'addan Boko Haram ya baƙunci lahira.
Jami'an tsaron sun kuma hallaka wasu miyagu tare da ƙwato makamai masu yawa a kokarin ganin an gama da 'yan ta'addan.
Dakarun sojojin sun hallaka kwamandan na Boko Haram ne bayan sun kai farmaki a maɓoyar ƴan ta'addan da ke cikin daji.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng