EFCC Ta Fadi Yadda Ta Yi da N50bn da Ta Kwato a Hannun Barayi

EFCC Ta Fadi Yadda Ta Yi da N50bn da Ta Kwato a Hannun Barayi

  • Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, ta yi bayani kan N50bn da ta ƙwato a hannun masu laifi a 2024
  • EFCC ta bayyana cewa ta sanya kuɗaɗen ne waɗanda ta ƙwato a hannun ɓarayin gwamnati da masu zamfa a asusun ba da lamunin karatu
  • Hukumar EFCC ta bayyana shekarar 2024, a matsayin lokacin da ta fi samun nasarar ƙwato kuɗaɗe a hannun masu laifi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta bayyana yadda ta yi da sama da Naira biliyan 50 da ta ƙwato daga masu aikata zamba a shekarar 2024.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa ta zuba kuɗaɗen ne a asusun ba da lamunin karatu na ƙasa (NELFUND).

EFCC ta yi bayani kan N50bn da ta kwato
EFCC ta sanya N50bn a asusun NELFUND Hoto: @EFCCNigeria
Source: Facebook

Jaridar Tribune ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin rahoton ƙididdiga na EFCC na shekarar 2024, wanda aka fitar ga manema labarai a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Za a koma gidan jiya: NNPCL ya dauki matakin da zai sa fetur ya yi tsada

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta kafa NELFUND

An kafa NELFUND ne bisa ga dokar ba ɗalibai lamuni ta shekarar 2024, wacce Shugaba Bola Tinubu ya rattaɓawa hannu a ranar 3 ga watan Afrilu, 2024.

Wannan shiri wata manufa ce da gwamnatin tarayya ta ƙirƙiro domin kawar da matsalolin kuɗi da ke hana ɗalibai samun ilmi a matakin gaba da sakandare.

A cikin rahotonta, EFCC ta bayyana ayyukanta a shekarar 2024 a matsayin mafi girman nasarorin da ta samu, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

EFCC ta ce shekarar 2024 ita ce shekarar da ta fi kowace shekara yawan ƙwato kuɗaɗe tun bayan kafuwarta a 2003.

Ina EFCC ta kai N50bn?

Ƙididdigar ta nuna cewa Naira biliyan 50 da gwamnatin tarayya ta bayar ga NELFUND, an samo su ne daga kuɗaɗen da EFCC ta ƙwato daga hannun ɓarayin gwamnati da masu aikata zamba.

"Shirin ba da rancen zai bai wa ɗalibai damar kammala karatunsu, su bayar da gagarumar gudunmawa ga ƙasarsu, tare da tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka ƙwato sun amfanar da ƴan Najeriya kai tsaye."

Kara karanta wannan

Abin da gwamnati ta ke yi a kudin da aka karbo daga hannun barayi Inji EFCC

"Ta hanyar samar da lamunin karatu, EFCC ba kawai tana tallafawa ilimi ba ne, har ma tana ƙarfafa matasan Najeriya domin su zama mutane masu amfani ga al’umma."
"Wannan mataki yana nuna jajircewar hukumar wajen inganta ci gaba mai ɗorewa a Najeriya."

- Wani ɓangare na rahoton EFCC

Meyasa EFCC ta samu nasarori a 2024

Hukumar ta danganta nasarorin da ta samu kan jajircewar jami’anta da kuma kyakkyawan yanayin aiki da shugabanninta da abokan huldarta suka samar.

Rahoton ya kuma tabbatar da aniyar EFCC na ci gaba da inganta ilmi da ƙwarewar lauyoyinta wajen tuhumar masu laifi.

Haka kuma, hukumar ta sake nanata ƙudirinta na yin aiki tare da hukumomi daban-daban da ƙasashen duniya domin ƙarfafa dabarun ƙwato dukiyoyin da aka samu ta haramtacciyar hanya.

EFCC ta cafke Udom Emmanuel

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta cafke tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel.

Hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamnan ne bisa zargin almundahanar kuɗaɗe waɗanda suka kai N700bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng