Jami'an Tsaro Sun Yi Taron Dangi kan Ƴan Bindiga a Adamawa, An Ceto Wasu Malamai

Jami'an Tsaro Sun Yi Taron Dangi kan Ƴan Bindiga a Adamawa, An Ceto Wasu Malamai

  • Jami’an tsaro sun kubutar da fastoci biyu da aka sace a Numan, jihar Adamawa, bayan hadin gwiwa tsakanin ‘yan sanda, DSS da ‘yan banga.
  • An sace fastocin; Abraham Samman da Matthew Dusami a karshen Fabrairu, a kauyen Gwaida Mallam, inda 'yan bindigar suka nemi kudin fansa
  • Bayan makonni ana tattara bayanai, jami’an tsaro sun gano maboyar ‘yan bindigar sannan suka kai samame da yammacin ranar Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Adamawa - Jami’an tsaro sun kubutar da wasu fastoci biyu da aka sace a jihar Adamawa bayan kai samamen hadin gwiwa tsakanin ‘yan sanda, DSS da ‘yan banga.

'Yan bindiga sun sace fastocin; Abraham Samman da Matthew Dusami, a ranar 21 ga Fabrairu a kauyen Gwaida Mallam, da ke karamar hukumar Numan.

Majiyar tsaro ta yi bayanin yadda aka kubutar da wasu malaman addini da aka sace a Adamawa
'Yan sanda, DSS sun kubutar da wasu malaman addini 2 a Adamawa bayan farmakar 'yan bindiga. Hoto: Getty Images
Asali: Twitter

Sojoji sun kubutar da fastoci a Adamawa

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa cikin gida a Kano, sun yi ta'asa bayan cirewa wani ƴan yatsu

Kafin a kubutar da su, masu garkuwar sun bukaci kudin fansa masu yawa, lamarin da ya haifar da fargaba a tsakanin ‘yan uwa da mabiya cocinsu, inji rahoton Zagazola Makama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makama ya bayyana cewa jami’an tsaro sun kai samame sansanin ‘yan bindigan da misalin karfe 5 na yammacin ranar Asabar, 8 ga watan Maris.

Binciken sirri ya nuna cewa an shafe makonni ana sa ido da tattara bayanai kafin jami’an tsaron su gano maboyar masu garkuwa da mutanen.

"Mun bi sawu kuma muka gano inda suka boye a kauyen Gwaida Mallam, sannan muka kai samame bayan kammala tattara bayanai," inji wata majiyar tsaro.

An cafke daya daga cikin masu garkuwar

A yayin farmakin, jami’an tsaro sun yi kokari don tabbatar da cewa ba a cutar da mutanen da aka sace yayin kokarin kubutar da su ba.

Rahoton ya tabbatar da cewa jami’an tsaron sun samu nasarar kubutar da malaman cocin biyu ba tare da daya daga cikinsu ya samu ko kwarzane ba.

Kara karanta wannan

Bayan alkawarin gwamna kan miyagu, jami'an tsaro sun hallaka jagoran Lakurawa

Wani daga cikin wadanda ake zargi da garkuwar, Tahamado Demian, wanda ke halartar tarukan cocin Katolika da malaman ke jagoranta, ya tsere yayin farmakin.

Sai dai daga bisani, jami’an rundunar Scorpion Squad sun cafke shi a Jimeta da misalin karfe 8:30 na yammacin ranar da aka kubutar da fastocin.

An kaddamar da bincike don gano sauran

Jami'an tsaro sun kubutar da wasu malaman addini da aka sace a jihar Adamawa
Malaman addini a jihar Adamawa sun shaki iskar 'yanci bayan jami'an tsaro sun kubutar da su. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jami’an tsaro sun garzaya da fastocin zuwa asibitin koyarwa na Modibbo Adama da ke a birnin Yola don duba lafiyarsu bayan shakar iska daga hannun ‘yan bindigar.

Sashen yaki da garkuwa da mutane na 'yan sanda ya ce ana ci gaba da bincike don gano sauran masu hannu a lamarin da kuma yadda aka kitsa sace su.

Hukumomi sun tabbatar da cewa ana kokarin kama duk wanda ke da alaka da ‘yan bindigan tare da rushe shirin su gaba daya.

‘Yan bindiga sun kai hari jihar Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan bindiga sun farmaki kauyen Zakirai, a karamar hukumar Gabasawa da ke jihar Kano, inda suka sace matashi dan shekara 20.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun dura Zamfara, sun dauki alhakin kai harin da ya kashe mutane 11

Maharan uku dauke da bindigogi da adduna sun shiga gidan wani mutumi mai suna Yusha’u Ma’aruf da misalin karfe 2:15 na dare, inda suka yi ta’adi.

An ce sun yi wa dansa Abubakar Yusha’u rauni ta hanyar sare yatsarsa, sannan suka sace wani daga cikin ‘ya’yansa, Mohammed Bello Yusha’u.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.