Shehu Sani Ya Yabi Tinubu, Ya Fadi Laifin da Buhari Ya Yi Wa Arewa a Shekara 8

Shehu Sani Ya Yabi Tinubu, Ya Fadi Laifin da Buhari Ya Yi Wa Arewa a Shekara 8

  • Sanata Shehu Sani ya yi magana kan salon mulkin gwamnatocin Shugaba Bola Tinubu da Muhammadu Buhari
  • Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya fi Buhari ƙoƙari wajen ɗaukar matakan samar da tsaro
  • Shehu Sani ya nuna cewa Muhammadu Buhari bai yi wa yankin Arewa wani abin a zo a gani ba, a shekara takwas da ya yi kan mulki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya kwatanta gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta Muhammadu Buhari.

Shehu Sani ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya fi tsohon shugaban ƙasa Buhari ƙoƙari a fannin samar da tsaro.

Shehu Sani ya yabi Shugaba Tinubu
Shehu Sani ya ce Tinubu ya fi Buhari kokari wajen samar da tsaro Hoto: @aonanuga1956, @ShehuSani, @BuhariSallau1
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta rahoto cewa tsohon sanatan ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai a ranar Lahadi a Abuja.

Kara karanta wannan

Daga shigarsa APC, Shehu Sani ya fara kalamai kan takarar Uba Sani a 2027

Shehu Sani ya caccaki Buhari

Yayin da yake bitar halin tsaro a ƙasar nan, musamman a Arewacin Najeriya, Shehu Sani ya ce an samu ci gaba idan aka kwatanta da zamanin Shugaba Muhammadu Buhari.

"Dole ne na faɗi cewa matakan tsaro na Tinubu sun fi na tsohon Shugaba Muhammadu Buhari sau 1,000."
“Babban matsalar Arewa ita ce namu (Buhari) ya yi mulki na tsawon shekaru takwas, amma bai aiwatar da manyan ayyukan da ake buƙata ba."
"Ayyukan wutar lantarki na Mambilla, yashe Kogin Neja, tashar jiragen ruwa ta Baro, da shawo kan matsalar tsaro a Arewacin Najeriya duk an bar su ba a kammala ba."
“Duk da haka, Buhari ya naɗa ƴan Arewa a matsayin shugabannin duk hukumomin tsaro na ƙasa, amma duk da haka an ci gaba da yankawa da kashe mutanenmu."
“Akwai manyan hanyoyi huɗu da ke haɗa jihohin Arewa da Abuja, Lokoja-Abuja, Kaduna-Kano-Abuja, Keffi-Abuja, da Minna-Suleja-Abuja. Ko ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi ba a kammala su ba a cikin shekaru takwas na mulkin Buhari.”

Kara karanta wannan

Seyi Tinubu da Minista sun dira gidan Buhari a Kaduna, an yada bidiyon

- Shehu Sani

Shehu Sani ya nuna mamakinsa kan dalilin da ya sa wasu ƴan Arewa ke sukar Tinubu a yanzu, alhali sun yi shiru a zamanin Buhari.

“Da an ɗauki matakan da suka dace a gwamnatin da ta gabata, da ba a shiga cikin yawancin matsalolin da ƙasar nan ke fuskanta a yanzu ba."

- Shehu Sani

Shehu Sani ya ba Tinubu shawara

Duk da haka, tsohon mai rajin kare haƙƙin bil’adama, wanda yanzu ya zama ɗan siyasa, ya buƙaci shugaban ƙasa da ya tabbatar da cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi suna la’akari da wahalhalun da jama’a ke fuskanta.

"Ƴan Najeriya na cikin wahala, suna fuskantar ƙuncin rayuwa. Dole ne a samar da matakan rage musu raɗaɗi."
“Mutane na fama wajen biyan kuɗin makaranta, masu gidaje sun ƙara kuɗin haya. Ya kamata gwamnati ta shigo don tallafawa ɓangaren ilmi da gidaje."
"Ya kamata a inganta asibitocin koyarwa ta yadda ƴan ƙasa ba za su dogara ga cibiyoyin lafiya marasa inganci ba."

Kara karanta wannan

"Ɗan takara 1 tal gare mu," Sanatan APC ya hango wanda zai ci gaba da mulkin Najeriya a 2027

- Shehu Sani

Shehu Sani ya goyi bayan Uba Sani

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya nuna goyon bayansa ga takarar Uba Sani a zaɓen 2027.

Shehu Sani ya bayyana cewa zai yi farin ciki idan Uba Sani ya koma mulkin Kaduna a wa'adi na biyu a shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng