Ana Wata ga Wata: 'Yan Bindiga Sun Shiga Kano, 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki
- Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sanar da samun nasarar cafke wasu mutane huɗu da ake zargin ƴan bindiga ne
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ya bayyana cewa an cafke mutanen ne bayan an samu bayanan sirri kan ayyukansu
- Mutanen da aka cafken, sun shigo ne daga jihar Katsina mai makwabtaka da Kano domin siyan bindiga ƙirar AK-47
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane huɗu da ake zargin ƴan bindiga ne.
Ƴan sandan sun cafke mutanen waɗanda rahotanni suka nuna cewa suna ƙoƙarin siyan bindiga ƙirar AK-47.

Asali: Original
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna, ne ya tabbatar da kama mutanen a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, a shafinsa na Facebook
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan sanda suka cafke ƴan bindiga

Kara karanta wannan
Dakarun sojoji sun kai dauki bayan 'yan bindiga sun farmaki mutane, sun samu nasara
A cewarsa, rundunar ƴan sandan ta samu gagarumar nasara a ƙoƙarinta na daƙile shigowar ƴan bindiga da sauran laifuka makamantan hakan a jihar.
"A ranar 6 ga watan Maris, 2025, da misalin ƙarfe 2:00 na rana, wata tawagar ƴan sanda ƙarƙashin jagorancin SP Ahmad Abdullahi, jami’in da ke kula da ofishin Jar Kuka, Kano, ta cafke wasu mutane huɗu da ake zargin ƴan bindiga ne a gidan mai na Chula, unguwar Hotoro."
"Waɗanda aka kama sun haɗa da Shukurana Salihu, mai shekaru 25, Rabi’u Dahiru, mai shekaru 35 da Ya’u Idris, mai shekaru 30, duk daga jihar Katsina, da kuma Muktar Sani, mai shekaru 30, daga unguwar Yandodo Hotoro, Kano."
"An kama su ne bisa sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa sun zo Kano da niyyar siyan bindiga ƙirar AK-47."
- SP Haruna Abdullahi Kiyawa
Ya ce an samu wannan nasarar ne bisa umarnin Sufeto Janar na ƴn Sanda, IGP Kayode Egbetokun, ga dukkan rundunonin ƴan sanda da sassan tsaro na musamman, na ɗaukar matakan da suka dace don murƙushe ayyukan ta’addanci.
An ƙwato kayayyakin laifi a hannunsu
Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa bayan gudanar da cikakken bincike, an samu kayayyakin laifi a hannunsu.
Kayayyakin sun haɗa da Bindigogi ƙirar guda uku, alburusai guda 12, wuƙaƙe guda huɗu, adda guda ɗaya.
Sauran sun haɗa da tsabar kuɗi N1,028,800m da wasu kayayyakin sihiri.
Abdullahi Haruna ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi a sashen binciken manyan laifuka na rundunar, kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.
Sanarwar ta kara da cewa:
"Wannan nasara wata shaida ce da ke nuna yadda rundunar ke jajircewa wajen daƙile shigowar ƴan bindiga da miyagun laifuka a Kano."
"Muna gode wa jama’a bisa goyon baya da haɗin kai da suke ba mu a ƙoƙarinmu na tabbatar da doka da oda a jihar."
Ƴan sanda sun yi ram da jami'an NDLEA
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke wasu jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA).
Ƴan sandan sun cafke jami'an na NDLEA ne guda biyu bisa zargin harbe wata yarinya ƴar shekara 19 har lahira.
Asali: Legit.ng