Akpabio Ya Kasa Hakura, Ya Yi Magana Mai Zafi kan Zargin Lalata da Matar Aure
- Shugaban majalisar dattawa ya nuna rashin jin daɗinsa kan zargin da Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi masa na cin zarafinta
- Godswill Akpabio ya bayyana cewa zargin da Sanata Natasha ta yi masa, ya sanya majalisa ta samu kanta cikin wani irin hali
- Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa ko a baya Sanatar Kogi ta tsakiya ta sha yin zargi na ƙarya kan cin zarafinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sake yin magana kan rikicin da ake tafkawa a majalisar a ƙarƙashinsa.
Sanata Godswill Akpabio ya bayyana halin da majalisar ta samu kanta a cikin sakamakon zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi masa.

Asali: Facebook
Godswill Akpabio ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wajen bikin ranar mata ta duniya, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin Natasha kan Akpabio ya tayar da ƙura
Majalisar dattawa dai ta kasance a cikin cece-kuce tun bayan da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi zargin cewa Akpabio ya yi mata cin zarafi ta fuskar neman lalata da ita, zargin da ya fito ya musanta.
Sanatar ta gabatar da takardar koke a kan Akpabio, amma kwamitin ladabtarwa na majalisar ya yi watsi da ita, sannan ya ba da shawarar dakatar da ita.
Matakin da majalisar ta ɗauka ya haifar da martani daban-daban, inda wasu mutane da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam suka buƙaci Akpabio da ya sauka daga muƙaminsa don a gudanar da bincike.
Me Akpabio ya ce kan zargin lalata da Natasha
Da yake magana a wurin taron, Akpabio ya ci gaba da musanta zargin, yana mai cewa duk zarge-zargen da Natasha ta taɓa yi a baya kan cin zarafi sun kasance ƙarya ne.
"Jiya na fahimci cewa abin da muke magana a kai ya faru ne kawai lokacin da aka canja kujerarta. Nan ne rikici ya ɓarke, kuma aka fara jefa zarge-zarge iri-iri."
"Wannan canjin kujera da kuma canjin kwamitinta, abin da Sanatoci suka saba gani lokaci zuwa lokaci, shi ne ya haifar da wannan hargitsi."
‘‘Ana cewa hakan ya faru ne a ranar 8 ga Disamba, rana guda kafin bikin murnar zagayowar ranar haihuwata, wanda aka gudanar a filin wasa a shekarar 2023."
"Tun daga wannan rana, ban taɓa ji ba, matata ba ta ji ba, ba ɗan Najeriyan da ya ji, mijinta bai taɓa jin wani batu na cin zarafi ba har sai da aka canza kwamitinta da kuma kujerarta.’’
‘‘Shin kun taɓa tunanin irin wahalar da wannan mata ta jefa wasu mutanen da ta taɓa zarginsu a baya? Babu wanda aka taɓa tabbatar da zarginta har yanzu."
"Kun yi tunanin irin illar da hakan ya haifar ga majalisar dattawa ta 10 da kuma martabar majalisa saboda waɗannan zarge-zargen marasa tushe?"
"Ku kalli waɗannan kyawawan matan. Na sha haɗuwa da su a lokuta da dama. Shin na taɓa cin zarafin ɗaya daga cikinku? Ko waccan na tunanin ba ku da kyau ne?"
- Sanata Godswill Akpabio
Shugaban APC ya magantu kan dakatar da Natasha
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, Aliyu Bello, ya goyi bayan dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Aliyu Bello ya bayyana cewa dakatarwar da majalisar ta yi wa sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, abu ne wanda ya dace.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng