Ramadan: Malamin Musulunci Ya Soki Rufe Makarantu a Arewa, Ya Yi Tunatarwa

Ramadan: Malamin Musulunci Ya Soki Rufe Makarantu a Arewa, Ya Yi Tunatarwa

  • Babban limamin ƙungiyar Al-Habibiyyah Islamic Society, ya nuna rashin gamsuwarsa da matakin rufe makarantu
  • Imam Fuad Adeyemi ya bayyana cewa bai kamata wasu gwamnonin Arewa su rufe makarantu ba saboda ana yin azumi
  • Malamin addinin musuluncin ya nuna cewa ƙara dagewa ake yi a lokacin azumi ba zama ake yi a shantake ba da Ramadan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babban limamin ƙasa na ƙungiyar Al-Habibiyyah Islamic Society, Imam Fuad Adeyemi, ya yi magana kan rufe makarantu da wasu gwamnonin jihohin Arewa suka yi a watan azumin Ramadan.

Malamin addinin Musuluncin ya soki matakin gwamnatocin na jihohin Arewa da suka haɗa da Bauchi, Katsina, Kano, da Kebbi, na rufe makarantu na tsawon makonni biyar saboda azumin Ramadan.

Imam Fuad Adeyemi ya soki matakin rufe makarantu a azumo
Imam Fuad Adeyemi bai gamsu da rufe makarantu a Ramadan ba Hoto: Lawal Muazu Bauchi, bba Kabir Yusuf, Nasir Idris
Source: Facebook

Imam Fuad Adeyemi ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Inside Sources' a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Wani bawan Allah ya faɗi ana tsakiyar sallah a masallaci, ya rasu a watan azumi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin musulunci ya soki gwamnoni

Ya ce watan Ramadan lokaci ne da Musulmi ke buƙatar su ƙara kusantar Allah tare da jajircewa a aikinsu.

Imam Fuad Adeyemi ya bayyana cewa rufe makarantu saboda azumin Ramadan, ba koyarwar addinin Musulunci ba ce.

"A gare ni, ina kallon hakan a matsayin siyasa. Idan ka san tarihin azumi a Musulunci, za su iya cewa akwai zafi, amma zafin da ke nan ba zai kai na Saudiyya ba."
A lokacin azumi, ana aiwatar da abubuwa da dama da ke canza yadda abubuwa ke gudana. Misali, lokacin da Musulmi suka yi ƙaura daga Makka zuwa Madina, akwai yaƙin da Larabawa suka kai musu da nufin su kawar da Musulunci gaba ɗaya."
"Larabawa sun zo da sojoji kimanin 1,000, amma Musulmi sun kasance kusan 313 ne kawai kuma ba su da makaman yaƙi. Wannan kuwa ya faru ne a lokacin azumi. Duk da haka, suka yi yaƙi, kuma suka yi nasara, mutum 313 suka yi galaba a kan mutum 1,000."

Kara karanta wannan

Yadda mutanen kabila baki daya suka musulunta a hannun Sheikh Saidu Jingir

“Abin da nake ƙoƙarin faɗa shi ne, Ramadan lokaci ne da ake maida hankali wajen komawa ga Allah. Ba lokaci ne na shaƙatawa ko jin daɗi ba, sai dai lokaci ne mai muhimmanci a rayuwar Musulmi."
"Don haka, wannan tunanin na rufe makarantu, a ganina, ba zan iya yarda da shi ba, ba na goyon baya, kuma ba koyarwar addinin Musulunci ba ne."
"Wannan shi ne karo na farko da na taɓa jin cewa an yi hutu saboda Ramadan. Haba don Allah, saboda me?"
"Ko a ranar Juma’a, Musulunci bai ce ka rufe shagonka gaba ɗaya ba, cewa ya yi ka fita ka yi aiki, kuma idan lokacin sallah ya yi, sai ka rufe shagonka, bayan ka idar da sallah, ka koma kasuwancinka."
"Musulunci addini ne da ke da ƙa’idoji, ba za ka iya tashi kawai ka ƙirƙiro wata sabuwar hanya ba."

- Imam Fuad Adeyemi

CAN za ta yi shari'a da gwamnonin Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta caccaki matakin wasu gwamnonin Arewa na rufe makarantu a lokacin watan azumin Ramadan.

Ƙungiyar CAN wacce ta nuna ɓacin ranta kan lamarin ta yi barazanar zuwa kotu idan gwamnonin ba su janye matakin da suka ɗauka ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng